Ganduje ya bai wa ɗan Kano tallafin karatu miliyan N3

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Kano, Umaru Abdullahi Ganduje, ya bada tallafin karatu na kuɗi Naira miliyan N3 ga wani matashin jihar, Suyudi Sani, saboda bajintar da ya nuna a jarrabawar neman shiga jami’a da hukumar JAMB ta saba shiryawa inda ya zama ɗalibin da ya fi kowa samun maki bayan da ya samu maki 303.

Gwamnatin Kano ta miƙa wa matashin cekin kuɗin ne ta hannun Kwamishinar Manyan Makarantun Jihar, Dakta Mariya Mahmud Bunkure, kuma tuni ya samu gurbin karatu a Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK), inji Kwamishinar.

Mariya ta ƙara da cewa, Suyudi ya nuna bajinta a gasar kimiyya daban-daban da ya halarta, manya da ƙanana.

Ta ce ganin burin zurfafa karatunsa da matashin ke shi ya sa Gwamna Ganduje ya sha alwashin tallafa masa wajen cim ma burinsa.

Ta ƙara da cewa, baya ga kuɗaɗen da aka bai wa Sayudi, gwamnatin jihar za kuma ta ɗauki ɗauniyarsa baki ɗaya don tabbatar da bai samu wata matsala ba.

Ta ce, gwamnati ta zaɓi yin haka ne don maida matashin abin koyi da kuma saka ƙaimi ga sauran ɗaliban jihar.

Sayudi ya nuna godiyarsa da cika alƙawarin da Gwamnatin Ganduje ta yi masa.