Barazanar hari: Amurka ta gargaɗi ‘ya’yanta mazauna Abuja

Daga BASHIR ISAH

Ofishin Jakadancin Amurka da ke Abuja, ya gargaɗi ‘yan Amurka mazauna birnin kan yiwuwar kai hare-hare a sassa daban-daban.

Gargaɗin na ƙunshe ne cikin saƙon da ofishin ya aika wa Amurkawa mazauna Najeriya mai ɗauke da kwanan wata 23 ga Oktoba wanda jaridar Neptune Prime ta samu gani.

Saƙon ya nuna hare-haren ka iya shafar wurare da dama, don haka ofishin ya ce zai taƙaita harkokinsa har sai abin da Allah Ya yi.

Daga nan, ofishin ya bai wa Amurkawa mazauna Najeriya shawarar kare kansu ta hanyar taƙaita tafiye-tafiye, guje wa shiga cinkison jama’a, tabbatar da cajin waya kowane lokaci saboda kiran gaggawa da sauransu.