Manoma sun yi asarar Naira miliyan 500 a Nasarawa – Ƙungiyar mata manoma

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Ƙungiyar Mata Manoma ta Ƙasa, reshen Jihar Nasarawa sun gudanar da taron manema labarai a birnin Lafiya a ranar Litinin da ta gabata domin tunawa da Ranar Abinci ta Duniya.

Da ta ke jawabi, Misis Juliet Sarki ta ce, a damunan bana mambobin ƙungiyarsu na manoma mata sun tafka asara sakamakon ambaliyar ruwa da aka samu a wasu sassan jihar Nasarawa.

Ta ce, ƙungiyar manoma mata masu yunƙurin samar da abinci a Nijeriya da ke jihar Nasarawa sun kai 70.

Ta qara da cewa, ambaliyar da aka samu a wasu sassan jihar Nasarawa ta yi sanadiyyar lalata amfanin gona na sama da Naira miliyan 500.

Ta yi kira ga Gwamnati da ta gaggauta kawowa manoma ɗauki domin samun gudanar da noman rani saboda al’umma su samu abinci, idan ba haka ba Allah kaɗai ya san halin da ƙasar za ta kasance a ciki.

Ta ƙara da cewa, gwamnati ta taimaka da takin zamani da maganin kwari da irin kayan shukawa da sauransu domin mambobin ƙungiyar da sauran ƙungiyoyin manoma su samu su gudanar da noma ta yadda za a samu abinci a Nijeriya.

Mambobin ƙungiyar da suka haɗu sun yi kiraye-kiraye ga Gwamnati da su duba yanayin da tarayyar Nijeriya ke ciki na matsalar abinci ga kuma asarar da aka samu bana a gonaki saboda ambaliyan ruwa.