Akwai buƙatar gwamnati ta riƙa tunawa da mata a shirye-shiryenta na noma —ASSAPIN

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugabar Ƙungiyar Ƙananan Manoman Nijeriya reshen Jihar Bauchi (ASSAPIN), Hajiya Amina Jibrin ta ce, ya kamata gwamnati ta riƙa sanya mata a jerin masu cin gajiyar shirye-shiryenta na noma domin samun sakamako mai kyau.

Hajiya Amina ta yi kiran ne a taron bikin ranar Abinci ta Duniya da aka gudanar a Bauchi.

Baya ga haka kuma, ta yi kira da a tallafa wa manoman, musamman a wannan lokacin, la’akari da yadda ambaliyar ruwa a bana ta sanya su asara.

Ta ƙara da cewa, kiran ya zamo dole domin manoman na buƙatar taimakon gwamnati da al’umma, wajen farfaɗo da nomansu, domin ta haka ne za su cigaba da samar da wadataccen abinci ga al’umma.

“Akwai buƙatar samar da dokoki da tsare-tsaren da za su bai wa ƙananan manoma damar samun inshora da kuma wayar da kansu kan muhimmancin hakan.

“Gwamnatin jiharmu ya kamata ta ƙirƙiri hukumar da za ta zaburar da mutane su yi noma, ƙarƙashin shirinta na cigaban ƙananan manoma”, inji ta.

Hajiya Amina ta kuma yi kira ga gwamnatin da ta ware kaso sittin na kasafin kuɗinta kamar yadda ya ke a yarjejeniyar Maputo da Gamayyar Ƙungiyar Ƙasashen Afrika AU ta yi a shekarar 2003.