Ranar Litinin za a koma karatu a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya

Daga MOH’D BELLO HABIB a Zariya

Mahukantar Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya sun sanar da komawa harkokin karatu a jami’ar ranar Litinin mai zuwa, wato 24 ga watan nan da muke ciki sakamakon janye yaji aikin da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa ta tsunduma a ciki har na tsawon watanni takwas.

Wannan na ƙunshe ne cikin wani ɗab’i na musamman da sashin al’amuran jama’a ta wallafa kuma aka raba wa manema labarai shekaranjiya.

Sanarwar ta ce mahukantar jami’ar sun cimma matsaya ne sakamakon taron gaggawa na Majalisar Ƙolin Jami’ar ta yi ranar Laraba 19 ga wannnan watan.

Sanarwa ta ci gaba da cewa a wannan zaman da majalisar ƙolin ta yi an amince da sauyin da aka samu na komawa harkokin karatu da majalisar ƙolin ta amince da shi na komawa na shekarar karatu na 2021/2022 a zama na 25 ga watan Nuwamban bara, saboda a lokacin ana cikin yajin aikin malaman jami’o’in.