Barazanar hari: Gwamnati ta rufe Kwalejin Kwali a Abuja

Daga BASHIR ISAH

Biyo bayan barazanar mahara a yankin babban birnin tarayya, Abuja, ya sa Gwamnatin Tarayya ɗaukar matakin rufe Kwalejin Tarayya (FGC) da ke Kwali a ranar Litinin don kauce wa jefa rayuwar ɗalibai da malamai cikin haɗari.

Gwamnati ta bada sanarwar rufe makarantar ne bayan da ta samu rahoton jami’an tsaro sun daƙile wani shirin kai harin da aka yi zargin ‘yan bindiga sun yi a yankin Bwari.

Wannan na zuwa ne kwanaki 21 bayan mummunan harin da ‘yan bindigar da ake kyautata zaton ISWAP ne suka kai gidan yarin Kuje a Abuja.

Lamarin da ya yi sanadiyar tserewar fursunonin ‘yan Boko Haram 68 daga gidan yarin.

Duk da dai an samu nasarar sake damƙe wasunsu da suka tseren, amma har yanzu ana zargin cewa wasunsu na nan ɓoye a sassan Abuja.