‘Yan Nijeriya na ci gaba da alhinin mutuwar jaruma Ada Ameh

Daga AISHA ASAS

Biyo bayan labarin mutuwar shaharariyyar ‘yar wasan Kudu, Ada Ameh, wadda ta ke cikin ganiyar ta a masana’antar finafinai ta Nollywood, ‘yan Nijeriya sun shiga alhini da kuma mamakin mutuwar jarumar wadda ta zo masu a ba-zata.

Jarumar wadda ta kasance ɗaya daga cikin jaruman da ke haska shirin nan mai dogon zango na ‘The Johnson’, ta mutu ne a ranar Lahadi, 17 ga watan Yuli, 2022, a asibitin da ke Jihar Delta inda aka kai ta, bayan ta yanke jiki ta faɗi a wani taro da ta halarta. Jarumar dai ta mutu tana da shekaru 48 a duniya.

A watan da ya gabata ne jarumar ta bayyana a cikin wata tattaunawa da aka yi da ita cewa, tana fama da rashin lafiyar ƙwaƙwalwa, wadda ta samu bayan mutuwa ta ɗauke ‘yarta, ‘yan’uwanta mata uku, ‘yan’uwanta maza uku da kuma mahaifinta.

‘Yan Nijeriya da dama ne suka wallafa a shafukansu na sada zumunta, kan irin yadda mutuwar ta jarumar ta tava zukatansu tare kuma da bin gawarta da addu’a. A ɓangaren jarumai na masana’antar Nollywood su ma ba a bar su a baya ba wurin ambato jarumar a shafukansu tare da nuna muhimmancinta a masana’antar.

Mai karatu zai iya tuna jaruma Ameh a duk lokacin da ya tuna da finafinai na Turanci na Kudu, musamman ma na nishaɗantarwa, kamar ‘Domitilla’, tsohon fim ne da aka ɗauka a shekara ta 1996, inda jarumar ta fito a matsayin Anita. Sai uwa-uba shirin fim ɗin ‘The Johnsons’, inda ta sace zuciyar ma’abuta kallon shirin.