Zaratan mawaƙa mata biyar na duniya da kuma arzikinsu

Daga AISHA ASAS

A wannan zamani baiwar waƙa ta wadatu ga mata fiye da inda aka fito, hakan ya sanya suka fara samun wurin zama na musamman a duniyar nishaɗantarwa, kasancewar su a gaba wurin samar da nishaɗi ta vangaren waƙa. Duniya ta san da zamansu hakan ya sa suka samu ɗaya daga cikin romon da shuhura ke bayarwa, wato dukiya.

Bincike ya nuna, yawaitar mata mawaƙa musamman a ɓangaren da ake kira ‘rapper’ ya taimaka ƙwarai wurin rage ƙalubalen da mata ke fuskanta a duniyar nishaɗantarwa. Domin sun yi ƙarfi kuma an fahimci harkar ba ta tafiya dole sai da su.

A yau shafin nishaɗi na jaridar al’umma, Blueprint Manhaja, zai shayar da masu karatu ɗan wani abu daga ƙoramar ilimi ta mawaƙa mata, inda za ku ji manyan mawaƙa biyar da duniya ta aminta da sun isa, da kuma tarin dukiyar da suke da ita.

  1. MC Lyte:
    Lana Michele Moorer, wadda aka fi sani da MC Lyte na ɗaya daga cikin manyan mawaƙan ‘Rep’ na duniya ta san da zamansu. Ta yi zamaninta ne a ƙarni na 80 yayin da ta fitar da tarin kuɗi na waƙoƙi. Mawaqiyar Amurka ce da ta ƙware a DJ da kuma ‘Rep’, ‘yar kasuwa kuma ‘yar shirin fim. Ta kasance ɗaya daga cikin sharararrun mata masu rera waƙar rep. da ta yi fice wajen nishaɗantar da mutane, kuma ta kasance mawaƙiyar mace ta farko da ta fara fitar da kuɗin waƙoƙi na karan-kai. Kazalika mace ta farko da ta ci satifiket ɗin zinari wato gold certification. Daga cikin waƙolinta akwai; ‘Paper Thin’, ‘Ruffneck’, ‘Cha Cha Cha’, ‘10% Dis’ da sauransu. Ƙiyasin kuɗinta kuwa, Dala miliyan takwas.
  2. Nicki Minaj:
    Duk wanda ya san Nicki ya san dole ne sunanta ya kasance a cikin wannan jerin matuƙar yana so ya gamsar da mai karatu, domin ita ce ake yi wa laƙabi da sarauniyar gambarar zamani, dalilin kasancewar gwana a fagen waƙa. Duniya ta fara amo da muryar Nicki a lokacin da ta fitar da kundin waƙoƙinta a shekara ta 2007 zuwa 2009. Waƙarta ta ‘Monster’ na ɗaya daga cikin bakandamiyarta sanadiyyar karɓuwa da ƙara mata masoya da ta yi. Wasu daga cikin waƙoƙinta sun haɗa da; ‘Super Bass,’ ‘Bang Bang,’ ‘Right By My Side,’ ‘Highschool,’ ‘Make Me Proud,’ ‘Your Love,’ ‘The Boys’ da sauransu. Ƙiyasin dukiyarta kuwa Dala miliyan tara.
  3. Lauryn Hill:
    Wannan mawaƙiya dai suraka ce ga sannanen mawaƙi Bom Marley, domin tana auren ɗanshi Steven Marley. An haifi Lauryn a ranar 26 ga watan Mayu, 1975, a garin New Jersey, Amurka. Ta kasance a jerin fitattun mawaƙiya sanadiyyar irin shuhura da ta yi, wanda hasashe ya nuna a lokacin da ta fito da kundinta na ‘The Miseducation of Lauryn Hill’ ne ya ƙara ɗaga darajarta a duniyar nishaɗantarwa.

Mawaƙiya ce da ta yi nasarar cin kambun karramawa na ‘Grammy Awards’ har sau takwas. Sannan tana cikin mawaƙan da suka yi nasarar amsar NAACP Award’. Wasu daga cikin waƙoƙinta sun haɗa da; ‘Ex-Factor’, ‘Doo Wop’, ‘Turn Your Lights Down Low,’ ‘Tell Him’ da sauransu. Ƙiyasin dukiyarta kuwa ita ce, Dala miliyan tara.

  1. Cardi B:
    Belcalis Marlenis Almánzar, wadda aka fi sani da Cardi B, sananiyyar mawaƙiyar Amurka ce kuma marubuciyar waƙa. Ɗaya ce daga cikin manyan mawaƙan da suka fito daga garin New York, kuma wadda ta yi fice a kafafen sada zumunta. Cardi B ta taɓa cikin kambun ‘Grammy Award’ inda albon ɗinta na ‘Invasion of Privacy’, ya zama zakaran gwajin dafi na shekarar. Kuma ta kafa tarihin zama mawaƙiyar ‘Rep’ ta farko da ta taɓa cin satifiket na daham, wato ‘ diamond-certified’. Wasu daga cikin waƙoƙinta sun haɗa da; ‘I Like It’, ‘Bodak Yellow’, ‘Bitter’, Drip’, ‘Pull Up’ da sauransu. Ƙiyasin dukiyarta ya kai Dala miliyan 40.
  2. Lil’ Kim:
    Kimberly Denise Jones, wadda aka fi sani Lil’ Kim a duniyar nishaɗantarwa. An haife ta a ranar 11 ga watan Yuli, 1974, a garin New York na Ƙasar Amurka. Kimberly na ɗaya daga cikin mawaqan da suka sha gwagwarmayar rayuwa, kuma suke da labarin da ya wuce mai ban tausayi. Kundin waƙoƙinta na ‘Hard Core’, wanda ta fitar a shekara ta 1996 ne ya fara ɗora ta a matakalan shuhura a fagen waƙa.

Duk da cewa, Denise ta samu tangarɗa a tafiyar shahararta ta sanadiyyar zaman da ta yi a kurkuku na tsayin shekara ɗaya, dalilin kamata da laifin yi wa kotu ƙarya kan harbin da ƙawarta ta yi. Sai dai fitowarta ke da wuya ta fitar da zafafan waƙoƙi da suka sace zuciyar ma’abuta sauraron waƙoƙi kuma suka ƙara mata shahara.

Queen Bee sunan da ta samu daga kafafen yaɗa labarai, ta yi waƙoƙi da dama, daga cikinsu akwai, ‘The Jump Off’, ‘Crush on You’, ‘Magic Stick’, ‘Big Momma Thang’ da sauransu. A ɓangaren dukiya kuwa Lil’ Kim na da dukiyar da ta kai dala miliyan ɗaya.