Bayan shafe sa’o’i 12 a filin jiragen sama na Libya, Super Eagles ta ƙi buga wasan nema gurbin AFCON

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A yau ne ƙungiyar Super Eagles ta Nijeriya ta yanke janyewa daga buga wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka (AFCON) da ƙasar Libya.

Lamarin ya auku ne bayan da jami’an gwamnatin Libiya suka jibge ƴan wasan na Super Eagles ba tare da tantance su ba har na tsawon awanni 12 a filin jiragen sama na Al-Abraq.

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa, NFF cikin wata sanarwa da ta fitar, ta ce hakan da aka yi wa ƙungiyar akwai haɗari duk da cewa an gano cewa filin an ware shi ne musamman don jigilar alhazai.

Sanarwar ta ce, hatta abinci da masauƙi Super Eagles ba ta samu ba wanda motocin da za su kai su masauƙin ma, su na da nisan sa’o’i uku daga inda su ke.

Duk da cewa NFF ta shirya motocin da za su yi jigilar ƙungiyar, hakan ya samu tasgaro sakamakon sauyin wajen sauka da jirgin nasu ya yi.

A sanadiyyar haka ne, ƴan wasan suka yanke shawarar janyewa daga buga wasan yayin da wakilan NFF suka shirya dawowa da ƴan wasan gida Nijeriya.

Har’ilayau, NFF ta shirya samar wa ƴan wasan otal ɗin da za su zauna inda ta yi ta nema a wurare mafi kusa, amma duk inda suka je sai a ce musu an bada umarnin kar da marabci ƴan Nijeriya.

“Jami’an jirginmu sun je neman ɗakuna a otal, amma su ma an faɗa musu irin abin da aka faɗa mana”, inji NFF.

Sannan, an bai wa Kyaftin ɗin ɗaki a otal saboda shi ɗan Arewacin Afirka ne, amma ya ƙi karɓa tare da zaɓar dawowa da sauran ƴan tawagar waɗanda suka yi bacci a cikin jirgin.

By Babaji