Ma’aurata sun mutu a hatsarin mota a Ogun

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wata babbar mota ta take wasu ma’aurata da wani mutum ɗaya a hanyar Sagamu-Ogijo da ke Jihar Ogun wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar su .

Lamarin ya auku ne a lokacin da mamatan ke cikin wata mota ƙirar Wagon da wani babur na Bajaj.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Omolola Odutola ta tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Lahadi cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta bayyana mijin mai suna Moses Ekpolo ɗan shekara 25 da matarsa, Josephine Ekpolo mai shekaru 19 da kuma wani Kolawole Moshood waɗanda likitoci suka tabbatar da mutuwar su a yayin da aka garzaya da su asibiti.

Kakakin ta ɗora laifin aukuwar hatsarin akan direban babbar motar wanda ta ce ya rikice ne a inda ya doki babur ɗin daga baya wanda shi kuma ya bugi motar ma’auratan tare da sauya musu akala.

Ta ƙara da cewa, bayan tabbatar da mutuwar su ne sai aka kai gawawwakin zuwa wajen ajiyar gawa na Idera da ke Sagamu.

Jami’ar ta kuma gargaɗi direbobi su ke tuki cikin nitsuwa da kuma bada tazara tsakanin su da ababen hawa musamman waɗanda ke maƙare da kaya.

By Babaji