Rahotannin da ke zuwa na nuni da cewa a halin yanzu hukumomin ƙasar Libya na tsare da tawagar Super Eagles na Nijeriya a filin jirgin saman Al Abaq da ke birnin Al Abaq.
Hakan ya biyo bayan karkatar da jirgin tawagar ne, mintuna kaɗan bayan ya sauka a Benghazi, inda nan ne dama zai sauka tun farko daga Abuja.
Super Eagles tare da wasu ‘yan ƙasashen waje da ke gudanar da ayyukansu a Turai a halin yanzu suna maƙale a filin tashi da saukar jiragen sama, kamar yadda wani faifan bidiyo da hukumar ƙwallon ƙafar Nijeriya NFF ta fitar.
Yanzu dai tawagar za ta yi tafiya ne ta hanya zuwa Benghazi, wurin da za a yi wasan, wanda zai kai tafiyar awa 3 da mintuna 30.
