Bayanai sun fito game da rahoton ba wa hammata iska tsakanin Ministan Harkokin Waje da Mataimakin Gwamnan Bauchi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wasu magoya bayan Mataimakin gwamnan Jihar Bauchi, Auwal Jatau, sun fitar da wasu bayanai da ke da alaƙa da bai wa hammata iska tsakanin sa da Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar.

Wani shaida daga zaman da suka gudanar da ya nemi a sakaye sunansa, ya ce batun cewa an casa Ministan ba gaskiya bane.

Ya ce, ministan mai motsa jiki ne wanda ya fi mataimakin gwamnan karsashi, ya na mai cewa ko faɗa aka yi da shi zai yi wahala a yi galaba akansa.

Don haka ya ce, batun an masa duka ba gaskiya bane, lamari ne da wasu da ke goyon bayan ɗaya ɓangaren suka ƙirƙira.

An fara samun tsama ne tsakanin ɓangarorin biyu a lokacin da magoya bayan Jatau suka yaɗa wasu kalaman tunzura akan ministan.

Lamarin ya yi ƙamari ne a lokacin da aka yi zargin mataimakin gwamnan da aibata mahaifin ministan, wanda ɗaya ne daga cikin manyan ƙasa.

By Babaji