An naɗa Hamza Sulaiman a matsayin Sadaukin Ƙasar Hausa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, ya naɗa shahararren mai tallafawa al’uma, hamshakin ɗan kasuwa, babban manomi, kuma jigon ɗan siyasa, Alhaji Hamza Sulaiman Faskari, a matsayin ‘Sadaukin Ƙasar Hausa’.

Bikin naɗin sarautar wanda ya gudana a fadar mai martaba Sarkin Daura, ya samu halartar dubun dubatar jama’a da suka haɗa da ‘yan siyasa, da magoya baya, da masoya, da ‘yan uwa da abokan arzikin Alhaji Hamza Sule.

Su ma abokan hulɗa da abokan arziki da ’yan siyasa daga maƙwabtan jihohi ba’a bar su a baya ba, jihohi kamar Kano, Kaduna, Zamfara, Jigawa, Sokoto, da Kebbi.

‘Yan siyasa daga shiyyar Funtua da suka haɗa da shuwagabannin jam’iyyar APC a matakin ƙananan hukumomi zuwa mazaɓu, da ‘yan majalisun tarayya da na jiha tsoffi da masu ci, da hakimai da dagatai da dama sun halarci bikin.

Jim kaɗan bayan ya naɗa ma Alhaji Hamza Sule rawanin, mai martaba Sarkin Daura Alhaji Umar Faruk Umar, ya ce masarautar ta yi la’akari ne da cancantarsa da irin sadaukarwar da ya yi wa Jihar Katsina a duk muƙaman da ya riƙe.

Sarkin ya ce majalisar ta kuma yi la’akari da irin taimakon da Hamza Sule yake ma al’uma, musamman gajiyayyu, da mabuƙata, da marayu da zawarawa, da matasa da mata, tare da ɗaukar nauyin karatun ɗaruruwan yara da iyayensu ba su da galihu.

“A matsayinsa na Kwamishinan Muhalli na Jihar Katsina, ƙoƙarin da ya yi ya sa jihar ta samu damar cin gajiyar shirin Bankin Duniya na NEWMAP, wanda ya aiwatar da ayyuka na biliyoyin Naira, kuma yanzu akwai wani aikin na Bankin Duniya da ake ci gaba da gudanarwa a ma’aikatarsa.

“A ƙarƙashin shirin an gina magudanan ruwa da dama a faɗin jihar waɗanda suka taimaka wajen shawo kan matsalar ambaliyar ruwa.

“Har ila yau waɗannan ayyukan sun magance matsalar zaizayar ƙasa da sauran ƙalubale na muhalli a faɗin jihar, kuma hakan ya ceto ƙauyuka da gonaki da dama daga zaizayewa.

“A nan ƙasar Daura sun dasa jeri-gwanon itatuwa waɗanda suka ƙawata mana ƙasar mu, Kuma suke taƙaita matsalar kwararowar hamada.

“Muna sane da irin gagarumar gudunmawar da Alhaji Hamza Sule ya bayar wajen kyautata zamantakewa da tattalin arzikin al’ummarmu, yana bai wa ɗalibai tallafin karatu, yana baiwa mata da matasa tallafi, yana taimakon gajiyayyu da marasa galihu, yana taimakon ‘yan gudun hijira da sauran makamantansu.

“Wannan ita ce hanyarmu ta yaba wa waɗannan da sauran ayyukan kishin ƙasa da Hamza Sule yake yi, kuma muna fatan hakan zai zama kwarin gwiwa a gare shi domin ya cigaba da ba da irin wannan gudummawar ga ci gaba da walwalar al’umma,” in ji Sarkin.

A jawabinsa na godiya ga wannan karimcin, Alhaji Hamza Sule ya godewa Sarkin bisa tabbatar masa da sarautar bisa la’akari da waɗannan dalilan, ya kuma yi alƙawarin ci gaba da biyayya ga masarautar ta Daura.

Ya ce ya tsunduma cikin ayyukan tallafa wa al’umma ne domin ya inganta walwalarsu kuma ya rage musu wahalhalun rayuwa, game da tallafa wa harkar ilimi da gina rayuwar matasa.

Alhaji Hamza Sule ya ce yana fatan waɗannan ayyuka na agaji za su Zama sadakatul jariya ga iyayensa waɗanda su suka ba shi tarbiyya da ilimin addini da na zamani.

Ya godewa manyan baƙi da sauran ‘yan uwa da abokan arziki da suka halarci bikin tare da yin kira garesu da su ci gaba da yi ma ƙasa addu’ar samun zaman lafiya da cigaba mai ɗorewa.

Alhaji Hamza Sule dai shi ne Kwamishinan Muhalli na Jihar Katsina, ya kuma riƙe muƙaman siyasa daban daban, kuma jigo ne na siyasa a shiyyar Funtua, da Jihar Katsina da shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya.

By ukarofi