Fadar Shugaban ƙasa ta mayar da martani ga Yusuf Datti Baba-Ahmed, mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a zaɓen 2023, bisa kalamansa da suka nuna shakku kan yiwuwar Shugaba Bola Tinubu sake samun nasara a zaɓen 2027. A wata tattaunawa da yayi a tashar Arise TV, Datti ya ce Tinubu bai kamata ya sake tsayawa takara ba idan yana da wayo, yana mai cewa dukkan alamu na nuna cewa APC za ta sha kaye a 2027.
Baba-Ahmed ya zargi Shugaba Tinubu da amfani da dabaru wajen tsayar da ‘yan takara tun daga shekarar 2007 har zuwa zaɓen da ya gabata. Ya ƙara da cewa jam’iyyar APC ta gaza cika alƙawura da ta ɗauka, yana mai jaddada cewa Buhari bai samar da tsaro ba, bai yaƙi cin hanci ba, haka kuma Tinubu ba zai iya ba. A cewarsa, lokacin sauyin shugabanci ya yi, kuma yan Najeriya za su haɗa kai domin kawar da jagoranci maras nagarta.
Sai dai a martanin da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare, ya fitar a shafinsa na X (Twitter), ya ce maganganun Datti ba su da tushe kuma cike suke da rashin fahimta. Ya ce Datti ya kasa fahimtar ainihin salon siyasa, yana mai cewa siyasa ba ta da alaƙa da tunanin ko ra’ayoyin marasa jajircewa. Ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu na samun nasarori masu amfani ta fuskar tattalin arziki, kuma IMF ta yaba da sauye-sauyen da gwamnatinsa ke aiwatarwa.
Sunday Dare ya bayyana cewa babu wani “makirci na siyasa” da zai hana Shugaba Tinubu nasarar sake lashe zaɓen 2027. A cewarsa, aikin da shugaban ƙasa ke yi zai buɗe masa hanya, kuma duk wani yunƙurin rage darajarsa ba zai yi tasiri ba. Ya shawarci Datti Baba-Ahmed da ya yi shiru ko kuma ya fice daga siyasa gaba ɗaya idan ba zai iya fafatawa da ‘yan siyasa na gaskiya ba.
