Bello ya rattaba hannu a wasu sabbin dokokin jiharsa

Daga AISHA ASAS

Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya sanya wa wasu sabbin dokoki guda biyu hannu.

Dokokin su ne, dokar gudanar da binciken sanin lafiyar masu shirin yin aure kafin ƙulla aure da kuma dokar haramta tada hankalin jama’a da abin da ya jiɓanci haka.

Taron sanya wa dokokin hannu ya gudana ne a Fadar Gwamnatin Jihar da ke Minna.

Da yake jawabi bayan kammala sanya wa dokokin hannu, Gwama Bello ya bayyana dokokin a matsayin masu muhimmancin gaske.

Bello ya yaba wa Majalisar Dokokin jihar bisa ƙoƙarin da ta yi wajen nazarin dokokin yadda ya dace har aka kai ga tabbatar da su a matsayin doka.

Ana sa ran cewa, da samuwar wannan doka ta haramta tada hankalin jama’a, za a samu raguwar aukuwar rikice-rikicen da suka shafi jinsi a jihar.

Hajiya Binta Mamman, mai wakiltar mazaɓa Gurara da Shaibu Liman Iya, mai wakiltar mazaɓar Suleja a majalisar dokin jihar, su ne ‘yan majalisun da suka haifar da waɗannan sabbin dokoki.

Duka waɗannan bayanai na ƙunshe ne cikin sanarwar manema labarai da ta fito daga hannun Sakatariyar Yaɗa Labarai ga Gwamnan Jihar, Mary Noel-Berje

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *