EFCC ta yi sabon shugaba

Daga FATUHU MUSTAPHA

A Larabar da ta gabata Majalisar Dattawan Nijeriya ta tabbatar da Abdulrasheed Bawa a matsayin sabon Shugaban Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa da Zambar Kuɗaɗe (EFCC).

Sanatocin sun shafe sa’o’i biyu suna tantance Bawa kafin daga bisani suka tabbatar da shi a sabon matsayin nasa.

Yayin da ake tantance shi, Bawa ya bai wa majalisar tabbacin cewa zai yi aiki tukuru don gyara wa hukumar zama ta hanyar inganta harkokinta kafin ƙarewar wa’adin jagorancinsa.

Bawa ya ce zai yi aiki tare da waɗanda suka dace a sassan duniya domin tabbatar da Nijeriya ta amfana da dukiyoyinta da aka sace.

Haka nan, ya sha alwashin cewa ya zuwa ƙarshen wa’adinsa hukumar za ta samu cigaba fiye da yadda ya zo ya tarar da ita.

Dangi, ‘yan’uwa da abokan arziki ne suka yi wa Bawa rakiya zuwa majalisar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *