Bikin Babbar Sallah: Masarautar Kano ta soke hawan daushe saboda korona

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Majalisar Masaurautar Kano ta ce ba za a gudanar da hawan Sallah ba yayin bikin Babbar Sallah na bana.

Majalisar ta ce an soke hawan ne domin cika umarnin gwamnati wajen yaƙi da cutar korona duba da cewa cutar ta kunno kai a karo na uku.

Madakin Kano, Alhaji Yusuf Nabahani ne ya sanar da hakan a wannan Litinin a  Kano.

Alhaji Yusuf ya ce Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, shi ne ya ba da umarnin a sanar da batun soke hawan ga masu ruwa da tsaki na masarautar.

Manhaja ta ruwaito Kwamitin Shugaban Kasa kan Yaƙi da Annobar Korona ƙarƙashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ta bayyana wasu jihohi guda shida ciki har da Kano, da ke fuskantar mummunan hatsarin annobar korona biyo bayan ɓullar wani nau’in ƙwayar cutar a Delta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *