Bikin raya al’adun Kaltungo na ƙara haɗin kai da zaman Lafiya – Mr Meso Dickson

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Gombe

An bayyana bikin raya Al’adun gargajiya da ake gudanarwa duk ƙarshen shekara a masarautar Kaltungo dake kuma Karamar hukumar ta Kaltungo a Jihar Gombe a matsayin bikin dake ƙara kawo zaman lafiya da haɗin kai matuƙa a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

Shugaban gabatar da taron na bana kuma shugaban rukunin Kamfanonin Mesoto Group, Mista Meso C.Dickson ya bayyana hakan yayin buɗe taron dake gudana na tsawon kwanaki biyu a masarautar.

Mista Meso ya bayyana godiyarsa ga Masarautar ƙarƙashin Mai Martaba, Mai Kaltungo Injiniya Saleh Muammad Umar mai tarin albarka tare da daɗaɗɗen Tarihi a kasa da ma Afirika baki ɗaya.

”wannan biki da ake gudanarwar a kowace shekara a wannan masarauta yana ƙara kawo haɗin kai da tabbatar da ba’a manta da Al’adu a ƙasar Gombe ba, ɗan haka yana da fa’ida sosai.”

Shugaban Taron ya jinjina wa Mai Kaltungo, da sauran dukkan masu-ruwa-da-tsaki musamman Alkyabbar Kaltungo, Hajiya Sa’adatu bisa namijin ƙoƙarinta wajen tabbatar da wannan taro.

A nasa jawabin, tsohon ministan yada labarai kuma Ƙyauren Nupe kuma ɗaya daga cikin masu fada aji a wannan ƙasa, Farfesa Jerry Gana ya bayyana jin daɗinsa bisa aika masa da goron gayyata.

Tsohon Ministan yaɗa Labaran ya ce fatansa shien a wannan lokaci shine Allah yakara ma Maikaltungo tsawon kwana yaci gaba da gudanar da ayukan alkhairin da yake gabatarwa.

Jerry Gana ya kuma ce ya sayi wasu daga cikin kwafin littafin da Mai Kaltungo ya ƙaddamar akan Naira milyan biyu.

Shi ma Ƙyauren Nupe ya bayyana cewa za su yi ƙoƙari wajen ganin an faɗaɗa hanyoyin samun ayyuka a Gwamnatin Tarayya a tsakanin al’umma.

Bikin ya hada wasu sarakunan gargajiya na Arewa maso Gabas da Yamma da ma ciki da wajen Najeriya gami da al’adu daban-daban da suke a wannan Masarauta.

By Babaji