
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Jihar Kwara, Frins Abdulƙadir Aliyu Mage ya rasu.
Marigayin ya rasu ne a asibitin koyarwa na Jami’ar Ilorin a yau Asabar, 28 ga watan Disamba.
Kawo yanzu gwamnatin jihar, ƙarƙashin jagorancin Abdurrahman Abdurrazak ba ta ce komai ba game da rashin.
A ranar 4 ga watan Nuwamba, 2024 ne aka rantsar da Frins Mahe a matsayin shugaban mai’aikatan wanda da farko shi ne sakataren gwamnatin.
Ya kuma taɓa riƙe muƙamin akawon Majalisar Dokokin jihar daga shekarar 2004 zuwa 2007.
Sannan ya taɓa zama ɗaya daga cikin jami’an tsohuwar Hukumar Wutar lantarki ta ƙasa (NEPA) da kuma Kamfanin Man fetur na Ƙasa (NNPCL).
