Bikin Sallah: Gwamnati ta ba da hutun kwana biyu

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Laraba, 28 da Alhamis, 29 ga Yunin 2023 a matsayin ranakun hutun gama-gari ga ma’aikata albarkacin bikin Babbar Salla (Eid-El-Kabir).

Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Oluwatoyin Akinlade, ya fitar.

Sanarwar ta ce, “Gwamnatin Tarayya ta bayyana Laraba, 28 da Alhamis, 29 ga Yuni, 2023 a matsayin ranakun hutu domin bikin Eid-el-Kabir.

“Kuma muna taya al’ummar Musulmi na gida da waje murnar bikin.”

Akinlade ya yi kira ga al’ummar Musulmi da ma ɗaukacin ‘yan Nijeriya da su yi sadaukarwa don cigaban ƙasa da al’ummarta.

Kazalika, ya bayyana yaƙini kan cewar, addu’o’i da yanke-yanken dabbobin da za a yi a matsayin ibada, za su taimaka wajen dawo da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *