
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Majalisar Ƙasa, NCS ta yi mubayi’a ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu inda ta ce ta na mai tabbatar da goyon bayanta ga shugabancinsa da kuma ƙoƙarinsa wajen daidaita ƙalubalen da ke fuskantar Nijeriya.
Majalisar wacce ta ƙunshi tsoffin shugabannin ƙasa da wasu manyan ƙasa, ta yaba wa hoɓɓasa da gwamnatin Tinubu ke yi na samar da hanyoyin rage raɗaɗi wa al’umma acikin matsanancin yanayi da ake ciki a faɗin ƙasar.
An gudanar da zaman ne a Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja wanda kuma shi ne na farko tunda shugaba Tinubu ya karɓi karagar mulki.
Cikin mahlarta taron akwai tsoffin shugabannin ƙasa kamar su Muhammadu Buhari da Goodluck Ebele Jonathan da Yakubu Gowon, yayin da Olusegun Obasanjo da Ibrahim Badamasi Babangida ba su samu halarta ba.
Hakan kuma, akwai wasu gwamnoni a taron irin su; Alex Otti na jihar Abia, Umo Eno na Akwa-Ibom da Ahmadu Fintiri na Adamawa, sannan sai Ministan Abuja, Nyesom Wike.
