Hukumar da ke yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa na Afirka sun bayyana annobar ƙyandar biri da ake fama da shi a Afirka ta tsakiya a mastayin abun fargaba. Hakan na faruwa ne bayan samun wani sabon nau’in ƙwayar cutar wanda ya ke da saurin yaɗuwa. Domin haka ne hukumar da ke yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ta Afirka ta bayar da sanarwa cewa lamarin ya zama annoba mai ɓukatar agajin gaggawa yayin da hukumar lafiya ta duniya ita ma a na sa ran za ta fitar da irin wannan sanarwar ranar 14 ga Agusta.
Masana na nuna damuwa kan yadda cutar ta ke yaɗuwa ganin yanzu ba a ƙauyuka kaɗai ba, har ma a birane da ke da yawan mutane, domin samun haka ka iya haifar da wata babbar annoba ga yankin Afirka ba ki ɗaya.
A watannin baya, an sami ɓullar cutar a wani gari da ake kira Bukavu,a ƙasar Congo. Sannan wasu ƙasashe kamar su Burundi,Kenya, Ugandan da Rwanda sun kawo rahoton samun cutar a karo na farko.
Nau’in cutar na wannan karon yafi haɗarin saurin yaɗuwa a kan nau’in cutar da ya jawo annobar da a akai fama da ita a shekarar 2022 duk duniya.
A dalilin haka ne, Ma’aikatar Lafiya ta Nijeriya tare da hukamar NCDC sun bada sanarwar duk matafiya da za su shigo Nijeriya daga Congo, ya zama wajibi su cike bayanan su a shafin matafiya da aka buɗe domin su tabbatar da yanayin lafiyar su.
