Buhari ya ɗauki Tinubu a matsayin barazana ga Nijeriya, inji Dr. Hakeem

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Jam’iyyar PRP na ƙasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce tsohon Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, bai goyi bayan miƙa mulki ga Bola Tinubu a 2023 da zuciya ɗaya ba, saboda yana ganin shugabancinsa zai iya zama matsala ga ƙasar.

Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne a wani taron da ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta shirya, inda ya soki gwamnatin Tinubu kan yadda yake ganin tattalin arziki da yanayin rayuwar ’yan Nijeriya suka tabarbare.

Ya ce furucin Tinubu na “Emilokan” a lokacin neman zaɓen 2023, wanda ke nufin “lokacina ne”, ya kamata ya sa ’yan Nijeriya su yi tambayoyi kan manufarsa ta neman shugabancin ƙasa.

A cewarsa, Buhari ya yi tsayayya da matsin lambar wasu da suka dage sai Tinubu ne zai gaje shi.

Baba-Ahmed ya zargi gwamnatin Tinubu da gazawa a muhimman fannoni na ƙasa, yana mai cewa bai kamata burin mutum ɗaya ya jefa makomar Nijeriya cikin haɗari ba.

Sai dai ya bayyana kwarin gwiwar cewa ’yan Nijeriya za su shawo kan ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta, kamar yadda suka tsallake matsaloli a baya.

Ya kuma bayyana cewa jam’iyyun adawa na ƙoƙarin haɗa kai domin samar da ɗan takara guda da zai fafata da Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Ya ce ƙungiyar haɗakar za ta samar da ɗan takara, yana mai kira ga masu adawa da sake zaɓen Tinubu da su goyi bayan duk wanda aka zaɓa ya wakilce su.

Baba-Ahmed ya kuma buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta tabbatar da cewa zaɓen 2027 zai nuna ainihin ra’ayin masu kaɗa ƙuri’a.

By ukarofi

Leave a Reply