Buhari ya ƙaddamar da sabuwar hanyar Nguru-Gashua-Bayamari a Yobe

Spread the love

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da buɗe sabuwar hanyar da Gwamnatin Tarayya ta kammala wadda ta tashi daga Nguru zuwa Gashua ta wuce Baymari tare da miƙa ta a hannun gwamnatin Jihar Yobe a ranar Lahadin makon jiya.

Da yake jawabi a madadin Shugaba Buhari a wajen taron buɗe hanyar, Ministan Wutar Lantarki, Abubakar D. Aliyu, ya bayyana aikin hanyar a matsayin ɗaya daga cikin muhimman ayyukan da Gwamnatin Tarayya ta gudanar a faɗin qasar nan domin bunƙasa harkokin sufuri da tattalin arziki a ƙasar nan.

Ya ce: “Kamar yadda za ku shaida, za mu miƙa wannan hanya mai tazarar kilomita sama da 55, wadda ta sada garuruwan Nguru-Gashua- Bayamari a Jihar Yobe zuwa jihohin Jigawa da Borno.

 “Har wala yau kuma, hanya ce mai matuƙar muhimmanci wadda za ta bunƙasa harkokin noma da kasuwanci a wannan yankin.”

A nashi ɓangaren, Minista a Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje ta Nijeriya, Babatunde Fashola, wanda Daraktan kula da manyan hanyoyi Mista Celestine Shuwusu ya wakilta ya bayyana farin ciki dangane da yadda ma’aikatar ta fara aikin kana ta kammala tare da miƙa shi cikin nasara.

Bugu da ƙari kuma, Mista Fashola ya yaba da cikakken haɗin kan ma’aikatar kuɗi ta tarayya, zauren majisar dokoki ta ƙasa, musamman shugaban kwamitin ayyuka na majisa bisa goyon bayan da suka bayar wajen kammala aikin. 

Haka zalika ya yaba wa ma’aikatansa, yan kwangila tare da yankunan da aka gudanar da aikin hanyar bisa haɗin kai da goyon baya. 

Da yake jawabi a bukin buɗe sabuwar hanyar, Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya bayyana ƙaddamar da buɗe hanyar a matsayin muhimmin tarihi ga al’ummar jihar saɓanin irin yadda cikin shekaru da yawa gwamnatocin baya suka mayar da jihar saniyar ware.

Bugu da ƙari, Gwamna Buni ya bayyana muhimmancin shimfiɗa hanyoyi wajen bunƙasa tattalin arziki da raya birane da yankunan karkara.

Haka zalika, Gwamna Buni ya yaba wa gwamnatin Muhammadu Buhari dangane da namijin ƙoƙari wajen dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.

A hannu guda kuma Buni ya jinjina wa sashen zartaswa dangane da amincewa da dawo wa da gwamnatin Jihar Yobe Naira biliyan 18 da ta kashe wajen gina hanyoyi mallakin Gwamnatin Tarayya.

By Editor