Daga BASHIR ISAH
Bayanai daga Ƙasar Angola, sun ce Allah ya yi wa tsohon shugaban kasar, Jose Eduardo dos Santos rasuwa.
Jaridar PM ta ruwaito cewar marigayin ya rasu ne a ranar Juma’a da misalin ƙarfe 11:10 na safe agogon Spaniya a wani asibitin Barcelona bayan da ya yi fama da rashin lafiya na dogon lokaci.
Santos ya mulki Ƙasar Angola na gomman shekaru inda ya bar duniya yana da shekara 79.
Fadar Shugaban Ƙasar ta sanar da rasuwar marigayin a shafinta na Facebook, inda ta bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga kasa da ma duniya baki ɗaya.
An bayyana marigayin a matsayin wanda ya ba da gudunmawa sosai wajen cigaban ƙasar a halin rayuwarsa.
