Buhari ya isa Senegal don halartar taron harkokin noma

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya isa Dakar, babban birnin Senegal, domin halartar Babban Taro Kan Harkokin Noma karo na biyu wanda ƙasar ta saba shiryawa.

Hadimin Shugaban mai kula masa da harkokin ɗaukar hoto, Sunday Aghaeze ne ya bayyana haka ranar Talata a wasu hotunan da ya ɗauka ya kuma wallafa.

Hotunan sun nuna yadda Ministan Shari’a na Senegal, Sidiki Kaba, ya tarbi Shugaba Buhari a filin jirgin sama.

Kazalika, hotunan sun nuna Shugaba Umaro Sissoco Embalo na Guinea Bissau ya gana da Buhari bayan isarsa ƙasar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), ya ruwaito cewar a ranar Talata Shugaba Buhari ya bar Legas zuwa ƙasar Senegal bayan kammala ziyarar aiki na kwana biyu a jihar inda ya ƙaddamar da wasu manyan ayyukan cigaban al’umma da gwamnatin jihar ta aiwatar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *