Bunƙasa ilimi: Zulum ya shigar da marayu 7,000 makaranta a Monguno a Jihar Borno

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Maiduguri

A ci gaba da ƙoƙarin sake farfaɗo da harkokin ilimi tare da ƙarfafa gwiwar jama’a wajen sake tsugunnar da yan gudun hijira a yankunan da rikicin Boko Haram ya tagayyra tare da samar da zaman lafiya ga al’umma, Gwamnan jihar, Farfesa Babagana Umara Zulum a ranar Litinin ya ziyarci Kasuwar Cross-Kauwa wadda a da sansanin ce ga mayaqan Boko Haram a ƙaramar hukumar Kukawa a Arewacin jihar Borno.

Garin Cross Kauwa mai tazarar kilomita 200 daga birnin Maiduguri, a arrwacin jihar kuma ya na kan gaɓar Tafkin Chadi.

Bugu da ƙari, Gwamna Zulum ya shigar da ya’yan yan gudun hijira da marayun da rikicin Boko Haram ya rutsa da iyayensu, kimanin 7000 zuwa makarantun boko a garin Monguno.

Ya ce gwamnatinsa ta na da kyakkyawan shirin faɗaɗa shigar da yara makarantun, wanda rijistar zai tashi daga 7,000 zuwa 10,000 nan gaba.

Gwamnan ya tabbatar wa da al’ummar yankin cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da baiwa jami’an tsaro dukkan goyon bayan da ya dace domin ganin an samu zaman lafiya a yankunan tare da shan alwashin sake buɗe kasuwanni idan abubuwa suka kyautata.

Har wala yau Gwamna Zulum ya jaddada cewa samar da abin dogaro da kai ga jama’a shi ne babban makami mai inganci wajen daƙile duk wani yunƙurin masu tayar da qayar baya. Yayin da ya sake jaddada cewa zama a sansanonin yan gudun hijira ba shi da wata ma’ana, don haka a tallafa wa mutane domin su samu abin dogaro da kai shi ne ya fi dacewa.

Haka kuma ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da ginawa tare da gyara waɗanda aka lalata da gine-ginen kananan hukumomi, da sake tsugunar da al’umma da inganta kasuwancin kan iyaka.

Gwamnan ya yaba wa ƙoƙarin gwamnatin tarayya a ƙarƙashin Shugaban ƙasa Muhammdu Buhari da kuma Rundunar Sojojin Nijeriya da sauran duk masu ruwa da tsaki waɗanda suka bayar da gudunmawa wajen samar da zaman lafiya a Jihar Borno.