Mawaƙan Annabi ba ‘yan bambaɗancin siyasa ba ne – Sharu Siddi Bolari

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

Shugaban Ƙungiyar Mawaƙan Annabi na Ƙasa (Ushaƙun Nabiyi Rasulil A’azam Nigeria), Sharu Auwal Siddi Bolari, ya ce mawaƙan bege masu ƙasidun yabon Manzon Allah ba ‘yan bambaɗancin siyasa ba ne.

Sharu Auwal Siddi Bolari, ya bayyana hakan ne a lokacin zantawarsa da wakilinmu a Gombe, inda ya ce bayan taron ƙungiyar na ƙasa da suka yi a Abuja sun yi irin sa a Kano sannan a makon da ya gabata sun yi wani a Maiduguri fadar Jihar Borno, inda suka ja hankalin matasa mawaqan Manzon Allah da cewa su kiyaye harshe kar kuma su bari ‘yan siyasa su yi amfani da su.

Ya ce taron na zaman lafiya ne da yi wa ƙasa addu’a, sannan ya yi kira ga mambobin ƙungiyar a ko’ina suke a faɗin Nijeriya da cewa su zama kamilallu domin duk mawaƙin Annabi ba kashin yasarwa ba ne kuma ba wulaƙantacce ba ne.

A cewarsa duk wani sha’iri dake begen Annabi kar dan yana waƙa irin na siyasa ya zama bambaɗo wajen son zuciya da kushe ko cin mutuncin wani hakan ba daidai ba ne.

Ya ƙara da cewa idan sha’iri zai dinga waƙarsa ta yabon Manzon Allah ya tsaya inda ya kamata kar son zuciya ta sa ya yi amfani da basirarsa ya zagi wani.

Sharu Auwal Siddi, ya qara jan hankalinsu sosai da cewa ganin mafi yawan su matasa ne su zama masu sana’a kar rashin abun yi ya sa a rinjaye su da wani abu su shiga layin ‘yan ta’adda ko ‘yan bangar siyasa, don haka su kiyaye.

Sannan sai ya yi amfani da damar ya yi kira ga shugabanni na sauran jihohi da su haɗa kai su nausa ƙungiyar gaba.

Daga qarshe sai ya ce yana da kyau kuma kowa ya mallaki katin zaɓe don zaɓar shugaban da yake ganin nagari ne zai masa adalci wanda rashin katin zaɓen zai sa ya gaza zabar shugaban da yake so.