Makarantar Halima Usman Zugarawa ta yaye ɗalibai 32

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano

Makarantar Islamiyya da karatun zamani da ake kira Halima Usman Memorial da ke ƙarƙashin shugabancin Marafan Dukajin Gaya Hakimin Wudil, Alhaji Abba wato Alhaji Yusuf Wakilin dukiya ya gina a garin Zugarawa da ke Ƙaramar Hukumar Wudil a Jihar Kano ta yi bikin yaye ɗalibai 32 a karo na farko a walimar bikin da aka yi a harabar makarantar da ke Zugarawa a ranar Lahadi da ta gabata ƙarƙashin jagorancin Dukajin Gaya Hakimin Wudil Alhaji Abba Muhammad.

A jawabinsa, Dukajin Gaya Hakimin Wudil Alhaji Abba Muhammad ya bayyana farin cikinsa da wannan rana mai muhinmanci musamman ganin yadda yara ƙanana suka sauke karatun Alƙur’ani Maigirma kuma wannan shi ne abun da Masarautar Gaya ke da buƙatar gani ko da yaushe na cigaban ilimin addini da na zamani da ma duk wani abu da zai kawo wa masarautar Gaya Kano da ma Nijeriya baki ɗaya.

Don haka ya yaba wa wanda ya assasa wannan makaranta ta tunawa da Halima Usman, da ke garin Zugarawa ƙarƙashin shugabanta kuma wanda ya assasa ta Alhaji Yusuf Wakilin Dukiya kuma Marafan Dukajin Gaya.

Alhaji Inusa Isyaku Lahadin Makole na daga cikin masu lura da wannan makaranta, ya ce wannan aiki na Marafa abun yabawa ne ganin yadda ake bada ilimin addini da na zamani dare da rana a wannan makaranta da Marafa ya gina, amma akwai buƙatar taimako daga duk wani mai ikon yi kamar yadda wanda ya assasata ya yi domin aikin alheri na kowa da kowa ne bana mutum ɗaya ba ne.

Alhaji Sadisu Ussaini Galadiman Zugarawa, wanda ya wakilci Dagaci Alhaji Balarabe Ɗanzoga, ya ce wannan haske ne babba da aka kawo wa Zugarawa, kuma Allah ya sanya taimako a wannan aiki na alkairi ya kuma karɓi aikin ga duk wanda ya bada gudunmawa na assasa wannan makaranta da cigabanta.