Ambaliyar ruwa ya ruguje gadar Katarko a Jihar Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu

Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a ranar Litinin ya jawo mummunan ambaliyar ruwan da ya ruguje Gadar-Katarko a Qaramar Hukumar Gujba a Jihar Yobe, wanda ta yanke hanyar Damaturu/Buni Yadi/ Biu; wadda ta haɗa jihar da jihohin Borno da Gombe, mai tazarar kilomita 22 daga Damaturu, babban birnin jihar Yobe.

Wanda zabtarewar gadar ya kawo cikas ga Ma’aikatan Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA) a ƙoƙarin kai wa jama’ar da ambaliyar ruwan ta shafa a ƙauyen Mutai a yankin, wanda suka gamu da mummunan ambaliyar ruwan da ya shafe garin baki ɗaya.

A wata sanarwar da Hukumar bayar da Agajin Gaggawa a Yobe (YOSEMA), Dr Mohammed Goje ya tabbatar da ambaliyar ruwan tare da bayyana cewa, Gadar- Katarko ta ruguje gaba ɗaya sakamakon ruwan sama mai ƙarfin gaske da ya malala zuwa yankin.

Dr. Goje ya ce, “wannan ita ce gada kuma titin daya tilo da ta hada Damaturu zuwa Gujba, Gulani da kananan hukumomin Biu.

“Haka kuma, wannan ambaliyar ruwa ya shafi al’ummar Mutai, Buni Yadi da Gulani wanda katsewar gadar zai ƙara kawo damuwa ga jama’a, musamman a ƙauyen Mutai.

“Hukumar SEMA a Yobe ta tuntuɓi sojoji domin samar da mafita ga al’ummar Katarko saboda yadda wasu jama’a ke yin dafifi a wurin don guje wa asarar rayuka.

“A hannu guda kuma, wannan na iya shafar tallafin gaggawa da muke kai wa jama’ar don ceton rayuwar al’ummar da ambaliyar ruwa ta shafa, sannan kuma gwamnatin jihar Yobe tana ƙoƙarin lalabo mafita wanda za ta taimaka wa waɗanda ibtila’in ya rutsa da su,” Dr. Goje ya bayyana.