Cacar baki ta kaure tsakanin gwamna da minista a gaban Buhari

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamnan Ribas, Nyesom Wike da ministan harkokin yankin Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio sun zagi junansu a kan siyasar jam’iyya a wani taron da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya halarta.

An gudanar da taron ne don bikin ƙaddamar da sashin kare ‘yan sandan Nijeriya na Muhammadu Buhari a hukumance wanda ya ƙunshi gidaje 68 da sauran kayayyakin aiki da hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC) ta gina a Fatakwal, jihar Ribas.

Mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osibanjo ne ya wakilci Buhari a wurin taron da mahalartansa suka haɗa da Wike, Akpabio, ministan harkokin ‘yan sanda, Muhammad Maigari Dingyaɗi; babban sufeton ‘yan sanda, Alƙali Usman; Shugaban kwamitin Majalisar Dattawa, Sanata Peter Nwaoboshi da takwaransa na Majalisar Wakilai, Olubunmi Tunji-Ojo da sauransu.

Akpabio ya tunzura buzu lokacin da ya kawo misali da rikicin jam’iyyar APC a matsayin dalilin da ya sa ba za su shiga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar ba don yin kira ga Wike ya koma APC.

Da yake magana da Wike ya ce, “Ba zan shiga cikin wasu don in jawo ka zuwa APC ba. Muna da isassun matsaloli a APC da ma.”

Ministan, yayin da ya yi ishara da irin abubuwan da Tunji-Ojo ya kwarara wa Wike sakamakon rawar da ya taka a Ribas, duk da haka, ya juya baya yana mai cewa zai iya ayyana Wike a matsayin Gwamna mai aiki idan ya koma APC.

Ga Wike, ya ce, “Saboda har yanzu ba ka cikin APC, ba zan kira ka Gwamna mai yin aiki ba. Lokacin da ka zo APC, zan kira ka Gwamna mai aiki.”

Amma Wike, wanda ya mayar da martani nan da nan bayan Akpabio, ya yi mamakin dalilin da ya sa Ministan ya mayar da rantsuwar zuwa kamfen ɗin siyasa.

Gwamnan, yana tamaita rikice-rikicen da ke faruwa a cikin Jam’iyyar PDP da APC, ya ce, “ba zai bar inda ake fama da zazzaɓin cizon sauro ya tafi zuwa inda ake fama da cutar kansa ba.”

Ya ce, “Ina tsammanin mun zo ne don ƙaddamar da wannan aikin. Ban san me ya sa Akpabio ya mayar da maganar ta yaƙin siyasa ba. Na gwammace in zauna inda ake samun zazzaɓin cizon sauro zuwa inda ake fama da cutar daji. Za a iya magance zazzaɓin cizon sauro amma ciwon daji a mataki na huɗu ba shi da magani. Ba na son in mutu yanzu.”