Gudunmawar mu ga zaman lafiya da daidaita haƙƙoƙin juna

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Kowacce ranar 21 ga watan Satumba tana kasancewa ranar da al’ummar duniya ke bukin Ranar Zaman Lafiya ta Duniya, ƙarƙashin jagorancin Majalisar Ɗinkin Duniya, gwamnatocin ƙasashe, ƙungiyoyin sa kai da masu zaman kansu, na gudanar da taruka da wasu shirye shirye da suka shafi harkokin samar da zaman lafiya da ƙalubalen da rikice-rikice masu nasaba da ƙabilanci, bambancin addini da siyasa, ke haifarwa ga tsaron ƙasa, ci gaban al’umma da zamantakewa.

A bana bukin ranar ya mayar da hankali ne wajen duba yadda samar da daidaito tsakanin al’umma zai taimaka wajen inganta zaman tare da cigaban ƙasa, domin duba yadda gwamnatocin ƙasashe da masu riƙe da madafun iko, musamman ‘yan siyasa suke kula da haƙƙoƙin jama’arsu, da daidaita su wajen rabon ayyuka da harkokin cigaba, ba tare da nuna bambanci tsakanin su ba, da sunan siyasa ko ƙabilanci da addini.

A Afirka wannan ba baƙon abu ba ne, duba da yadda nuna bambance bambance a tsakanin ‘yan ƙasa ke haifar da ƙalubalen tsaro, rikice-rikicen ƙabilanci, ayyukan masu ta da ƙayar baya da ‘yan aware da ke ɗaukar makamai don bayyana rashin jin dazin su game da salon shugabanci ko danniyar azzaluman shugabanni, wanda dalilin hakan ake samun asarar rayuka da dukiyoyin al’umma.

Mun ga yadda zarge-zargen rashin adalci, danniya da rashin ba da damar cin moriyar albarkar da ake samu daga ayyukan ma’adinan ƙasa ya jefa wasu ƙasashe a yaƙin basasa da lalata ƙasa. Dubi dai misalin yaƙe yaƙen da aka yi a wasu ƙasashen Afirka irin su, Laberiya, Saliyo, Mali, Sudan, Ruwanda, Jumhuriyyar Dimokuraɗiyyar Congo, da Jumhuriyyar Tsakiyar Afirka da sauran fitintinu da ake fuskanta nan da can.

Mu ma a nan Nijeriya mun ga irin yadda tsageran Naija Delta suka riƙa haifar da asarar ɗimbin dukiyar ƙasa, dangane da yadda suka riƙa kukan ba a kula da su, da kuma zargin ana lalata musu muhalli sakamakon ayyukan kamfanonin haƙar man fetur da ke aiki a yankunan su. Amma saurin ɗaukar matakin da Gwamnatin Tarayya ta yi ya taimaka wajen shawo kan matsalar cikin taƙaitaccen lokaci. Duk kuwa da asarar rayuka da aka fuskanta a farkon tawayen.

Ko da fitinar ‘yan bindiga dake addabar shiyyar Arewa Maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, waɗanda ke kai hare hare a cikin gari da ƙauyuka, ana kashe-kashen rayuka, satar dukiya da garkuwa da mutane, akwai masu ganin wannan fitinar da ke zama babban ƙalubalen tsaro a ƙasa na da nasaba da rashin nuna kulawa da al’amarin mazauna karkara da makiyaya, duk kuwa da gudunmawar da suke bayar wa ga tattalin arziƙin ƙasa a nasu ɓangaren. Daga cikin masu irin wannan ra’ayi akwai babban malami Sheikh Ahmad Mahmud Gumi, da ke ganin akwai buƙatar gwamnati ta zauna da shugabannin waɗannan ‘yan bindiga, don kawo ƙarshen wannan ta’addaci cikin ruwan sanyi.

Ba ina nuna dacewa ko rashin dacewar wannan ra’ayi nasa ba ne, don na san masana harkokin tsaro da ƙwararru sun yi tsokaci game da haka. Amma manufar wannan rubutu shi ne bayyana yadda rashin adalci ga wani ɓangare na ‘yan ƙasa ke iya haifar da matsalar tsaro da rashin zaman lafiya. Saƙon da bukin Ranar Zaman Lafiya ta Duniya ya yi ƙoƙarin isarwa ga masu faɗa a ji na duniya.

Mutum ko a gidan sa ya ce, ba zai yi adalci a tsakanin iyalin sa ba to, babu shakka ya san sai ya gamu da ƙalubalen rashin kwanciyar hankali. Musamman idan matansa biyu ne ko fiye, haka ma kuma ko da a tsakanin yaransa na cikin sa ne. Adalci shi ne ginshiƙin samun ingantaccen zaman lafiya da cigaba.

Sau da dama akan samu rigingimu ne na cikin gida, sakamakon zargin ana mayar da wani sashi na ‘yan ƙasa a matsayin ‘yan bora wasu kuma ‘yan mowa. Duk lokacin da irin waxannan zarge-zarge suka fara bayyana, tun ana yin su a ɓoye har suka fara fitowa sarari to, babu shakka alamu ne da ke nuna akwai ɓoyayyiyar damuwa, da matuqar ba a shawo kanta da wuri ba kuma cikin hikima, za ta iya rikiɗewa ta zama matsala mai sarƙaƙiya.

Masana harkar samar da zaman lafiya suna ganin lallai ne a riƙa sa ido sosai da kai ɗaukin gaggawa a duk lokacin da aka fuskanci barazanar wata magana ko qorafi na yawo kuma yana ɗaukar hankalin jama’a. Musamman ‘yan siyasa da wakilan al’umma da ke cikin gwamnati, waɗanda yardar jama’a da quri’un talakawa suka kai su ga matakin da suke, su daina amfani da ofisoshin su suna nuna wariya a tsakanin jama’ar su, yayin gudanar da ayyukan cigaban al’umma ko rabon tallafi da sauran harkokin da tsarin siyasar dimukraɗiyya ya kawo, domin jin daɗin talakawa.

Kasancewar Nijeriya, a matsayin ƙasa mai yawan ƙabilu, da bambance bambance irin na ɓangaranci, siyasa da addini ya kamata ‘yan siyasa, da gwamnati su zama masu hattara wajen tabbatar da ganin an ja kowanne ɓangare na al’umma a kusa, da inda zai ɗanɗanon romon dimukraɗiyya, shi ma a share masa hawaye, ta hanyar biya masa buƙatun sa a matsayin sa na ɗan ƙasa. Ya samu damar shiga tsarin ba da tallafi ko bashin kuɗaɗen sana’o’in dogaro da kai. Ya samu damar aikin gwamnati, kamar kowa, kuma yankin sa ya samu damar ayyukan raya ƙasa da suka haɗa da hanyoyi, asibitoci, makarantu, da tsaro, ba sai don yana wata ƙabila, ko daga wani yanki, ko yana zaune a birni kusa da gwamnati ba.

Akwai wasu zarge-zarge da dama da ake yi wa wasu ‘yan siyasa, waɗanda ba sa yarda wani daga cikin jama’ar su ya fito takarar wani muƙami sai in daga vangare kaza yake, haka idan rabon wani kayan abinci ko tallafi za a bayar sai dai a gayyaci ‘yan wata jam’iyya, su za su ci moriyar aikin da ya kamata a ce na kowa da kowa ne.

Masu hikimar magana na cewa, ɗan hakkin da ka raina shi zai tsole maka ido. A dalilin zarge zargen nuna rashin adalci, tsirarun ƙabilu, aƙidu da wani yanki na jama’a, ana samun yunƙurin masu tada ƙayar baya, bore da tarzoma, waɗanda fitinar su ke hana masu ƙarfin iko, da rinjaye a cikin al’umma kwanciyar hankali da sukuni.

Ba ma kawai a kan gwamnati ko mahukunta ba, mu ma a karan kan mu akwai buƙatar mu kasance masu tsare gaskiya, mutunta haƙƙoƙin juna, da yin adalci a tsakanin mu. Masu ƙarfi da raunana, masu arziki da talakawa, maza da mata, manya da yara, malamai da ɗalibai. Duk wanda zama ko hulɗa ta haɗa mu tare to, mu aikata gaskiya, mu yi abin da ko bayan ba ma nan za a tabbatar da mun yi ƙoƙarin yin adalci, kuma matakin da muka ɗauka zai samar da tsaro, adalci da zaman lafiya.