Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya yabi rundunar sojin ƙasar da ta bayyana kama sojan da ake zargi da harbe wani matashi mai shekaru 16 a Zariya da ke Jihar Kaduna.
Atiku wanda ya yi wannan yabo cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba, ya kuma bayyana alhininsa kan yadda matashin ya rasa ransa.
Wazirin Adamawa ya ce akwai buƙatar a gudanar da bincike kan sauran zargin abubuwan da a jami’an tsaron suka yi a sassan ƙasar a lokacin zanga-zangar.
“Ina kuma kira da a gudanar da cikakken bincike a kan sauran ayyukan da sojoji, ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro suka yi a lokacin zanga-zangar.”
