Mafi yawa daga cikin masu zanga-zanga almajirai ne da ba su san manufar hakan ba – Gwamnan Nasarawa

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya buƙaci Arewa ta magance matsalolinta, ya na mai cewa mafi yawancin waɗanda ke yin zanga-zangar tsadar rayuwa a jihar Almajirai ne ba su san komai ba game da gangami.

Zanga-zangar wacce aka faro a ranar 1 ga watan Agusta, an fara ta ne cikin lumana wanda daga baya ta sauya salo sakamakon samun bayanan sata da lalata kadarorin gwamnati da na al’umma, saboda haka aka sanya dokar hana fita wasu jihohi.

“Mafi yawa daga cikin su ba su ma san ma’anar zanga-zanga ba. A lokacin da na yi magana da su, ba su san akane su ke zanga-zanga ba,” inji Sule.

Ya kuma ce ɗaya daga cikin hanyoyin magance matsalar jahilci a Arewa shi ne a ilimantar da al’umma, ya na mai cewa zanga-zangar hanya ce ta ankarar da ƴan siyasa a shiyyar wajen ninninka ayyukansu don magance matsalolin da ke addabar su.

Ya ƙara da cewa “ɗaya daga cikin matsaloli a Arewa daga ranar da na zo, shi ne batun ilimi wanda kuma shi ne mu ke ta ƙoƙari a kai har zuwa yanzu.”

By Babaji