Daga RABIU SANUSI
An buƙaci shugabannin jam’iyyu a Jihar Kano da su samar da ‘yan takarar da za su tsaya zaɓe a ƙananan hukumomin da zai gudana nan bada daɗewa ba.
Shugaban hukumar zaɓe na jihar Kano Farfesa Sani Lawan Malumfashi ne ya bayyana haka a yayin da yake ganawa da shugabannin jam’iyyu na jihar Kano a ranar Alhamis ɗin wannan makon.
Shugaban hukumar zaɓen ya ce a yanzu ne ya kamata jam’iyya ta samar da shugaban da zai kawo wa al’umma canjin da suke buƙata, waɗanda kuma za su taimaka wajen kawo ayyukan raya ƙasa da za su taimakama matakin gwamnatin jiha da ƙasa.
Farfesa Malumfashi ya ƙara da cewa wannnan ƙasar tamu tana da buƙatar shugabannin da za su kawo mata ɗaukin da zai taimaka matuƙa wajen haƙo ma’adanai da sauran alkhairai masu tarin yawan da ake da su a ƙarƙashin ƙasar nan.
Sai dai shugaban hukumar zaɓen ya ce hukumar su bata da alhakin da za ta zaɓa wa al’umma ɗan takara ko makamanci hakan, sai dai suna da damar da za su bada shawarwari da akan alamomin ɗan takara mai nagarta.
“Dole ku ba shugabannin da kuka tsayar shawara dan su yi wa al’umma aiki tuƙuru ba buƙatar kan su ba.
“Akwai ƙalubale mai tarin yawa akan ku shugabannin jam’iyya wajen tantace wanda zaku tsayar wa al’umma wakili na gari da zai kawo ɗauki ga buƙatun da suke da shi.
Sani Lawan ya kuma ja hankalin shugabannin jam’iyyun da cewa ya zama wajibi ‘yan takarar da aka tsaida su zama masu tsarkake kalamansu da amfani da tsarkakken harshe yayin yaƙin neman zaɓe.
