Canja fasalin Naira: ’Yan ta’adda sun fara karɓar kuɗin Nijar

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar ta’addancin ISWAP, ta haramta karɓar Naira daga hannun manoma da sauran jama’a, biyo bayan matakin da Gwamnatin Nijeriya ta ɗauka na canja fasali takardun kuɗin ƙasar.

Idan za a iya tunawa, a kwanakin baya ne dai Gwamnatin Nojeriya ta sanar da cewa ta yanke shawarar canja fasalin takardu na Naira 200 da 500 da kuma 1000, waɗanda za ta fara fitar da su nan da watan Disamba, sannan a ranar 31 ga Janairun 2023, za a daina karɓar tsoffin takardun.

Sai dai bayanai na nuna cewa wannan mataki ya jefa mayaƙan ISWAP a yankin Tumbus na tafkin Chadi da kuma nesanta daga rassan bankuna cikin ruɗani domin zai yi wuya su canja kuɗaɗensu zuwa sabbin takardun kuɗi duba da yawan kuɗaɗen.

Wata majiyar leƙen asiri ta shaida wa Zagazola Makama, ƙwararre kan yaƙi da tayar da ƙayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, cewa yanzu haka, ’yan ta da ƙayar bayan suna karɓar kuɗin CFA na ƙasashen rainon Faransa na Afirka ta Yamma da suke niyyar maye gurbin Nairar Nijeriya a matsayin kuɗin kasuwanci a yankin.

Majiyar ta kuma ce, ’yan ta’addan sun kuma haramta wa duk wasu masunta da makiyaya da manoma shiga cikin tafkin Chadi ta hanyar Marte da Abadam da kuma Gamborun Ngala, domin hana Naira shiga sansanonin ’yan ta’addan da ke Tafkin Chadi.

Ibn Umar da Malam Ba’ana, kwamandojin ’yan ISWAP masu kula da haraji da lauyoyi, waɗanda suka kafa dokar, sun ce an bar mutanen ne kawai ta hanyar aminci da ƙungiyar ta’addanci ta kafa ta Bulgaram, Cikka, Guma, Maltam, Doron, Liman da Ramin Dorina, wasu ƙauyuka a Jamhuriyar Kamaru.

A maimakon haka, ISWAP na karɓar CFA 1,500 a matsayin haraji kowane wata daga mutanen da suka nuna suna son biya.

Har ila yau, sun tabbatar da hanyoyin kasuwanci musamman don ba da dama ga ’yan kasuwar shigo musu da kayan abinci da man fetur da makamai da sauran kayan aiki.