Za mu fifita buƙatun mata a tsarin mulkinmu – Ruƙayya Atiku

Daga WAKILIYARMU

Uwargidan ɗan takarar Shugabancin Nijeriya, Alhaji Atiku Abubakar wato Gimbiya Rukayya Atiku Abubakar ta ce Muhimmancin da mata ke da shi ne, ya sa suka sanya musu jadawalin samar da muhimman abubuwan da za su taimaka musu a rayuwa musamman ɓangaren abinda ya shafi ilimi da lafiya dama fannin bunƙasa sana’o’i in dai Allah ya ba su mulki. 

Hajiya Ruƙayya ta yi wannan jawabin ne a yayin wata ziyara da ta kawo nan jihar Kano.

Ta kuma ƙara da cewa, tuni ta samar da cibiyoyin koyar da sana’oi don tallafa wa mata da bunqasa rayuwarsu da kuma cigabansu.

Wakiliyar mu ta rawaito cewa, tuni Wazirin Adamawa ya dukufa wajen tallafa wa matasa domin fitar da su daga Halin da suke ciki na rashin aikin yi.

Da take nata jawabin shugabar cibiyar wayar da kan mata a kan muhimmancin zaɓe da zaɓar shugaba nagari ta Grama Media Action Arewa, Malama Hadiza Balanti Chediyar ‘yan gurasa cewa ta yi uwargidan ɗan takarar Shugabancin Ƙasa Alhaji Atiku Abubakar wato Gimbiya Rukayya Atiku Abubakar ta ce muhimmancin da mata ke da shi ne, ya sa suka sanya musu jadawalin samar da muhimman abubuwan da zasu taimaka musu a rayuwa musamman bangaren abinda ya shafi ilimi da lafiya dama fannin bunkasa sana’o’i.

Hajiya Rukayya ta yi wannan jawabin ne a yayin wata ziyara data kawo nan jihar Kano.

Ta kuma kara da cewa tuni ta samar da cibiyoyin koyar da sana’oi dan tallafa wa mata da bunkasa rayuwar su da kuma cigaban su.

Wakiliyar mu Hadiza Balanti ta rawaito cewa tuni Wazirin Adamawa ya duƙufa wajen tallafawa matasa domin fitar da su daga Halin da suke ciki na rashin aikin yi.

Da take nata jawabin shugabar cibiyar wayar da kan mata akan muhimmancin zabe da zabar shugaba nagari ta Grama Media Action Arewa, Malama Hadiza Balanti chediyar ‘yan gurasa cewa ta yi, ta bayyana cewa, ɓangarensu sun daina yarda mata su fito cikin tsakar rana da yunwa da ƙishirwa su yi zaɓe, amma da zarar an ci zaɓe, sai a manta da su kwata-kwata.

Ta kuma qara da cewa “Mun bi saƙo da loko da lungu na unguwannin dake ƙwaryar Kano da suka haɗa da unguwanni 143, da wasu ɓangarori na ƙananan hukumomin dake jihar Kano, kan cewar a wannan karon mata kada su yarda da kuɗi ko daɗin baki na wasu ‘yan siyasar ko kuma rubuce-rubuce a takardu, sam, kar ku yarda.

“Mata, ku zaɓi jagora nagari wanda ya san darajar mata, kuma duk rintsi duk tsanani, ba zai manta da irin gudummawar da muka bayar ba”, inji Hadiza Balanti”.