Labarai

Ranar ‘Yan Mazan Jiya: Gwamnan Zamfara ya sha alwashin tallafa wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu

Ranar ‘Yan Mazan Jiya: Gwamnan Zamfara ya sha alwashin tallafa wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu

Daga BELLO A. BABAJI Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta cigaba da ƙoƙarin inganta rayukan iyalan jami'an sojojin da suka rasa rayukansu a bakin aiki. A lokacin da ya ke jawabi a taron ranar tunawa da ƴan mazan jiya ta 2025 a filin taro na Trade Fair dake Gusau, gwamnan ya sanar da bada tallafin Naira miliyan 20 ga iyalan sojojin na reshen jihar Zamfara. Kakakinsa, Sulaiman Bala Idris kamar yadda ya bayyana a wata takarda, ya ce gwamnan ya gabatar da tallafin ne a lokacin da ya ke ƙaddamar da buɗe taron na shekarar…
Read More
Cutar Murar Tsuntsaye: An buƙaci al’ummar Kano su kwantar da hankali

Cutar Murar Tsuntsaye: An buƙaci al’ummar Kano su kwantar da hankali

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Yayin da ake fargabar samun ɓarkewar annobar murar tsuntsaye a Kano, gwamnatin jihar ta buƙaci al’umma da su kwantar da hankalinsu tare da kai rahoton duk wani zargi da ake da shi game da cutar ga hukumomin da abin ya shafa. Raɗe-raɗin ɓullar annobar ya bayyana ne sakamakon wani rahoton da aka samu a watan Disamba na 2024 cewa wani matashi ɗan ƙaramar hukumar Gwale ya sayo agwagwa a kasuwar Janguza da ke ƙaramar hukumar Tofa ya haɗa ta da kajin da yake kiwo. Daga baya sai ya lura kajin sun fara nuna alamun matsalar…
Read More
Gwamnatin Katsina ta gurfanar da masu cin zarafin mata a kotu

Gwamnatin Katsina ta gurfanar da masu cin zarafin mata a kotu

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta gurfanar da masu cin zarafin mata da bil'adama a babban Kotun Tarayya dake jihar. Kwamishinar Shari'a ta jihar, Barista Fadeela Muhammad Dikko ta shaida wa manema labarai haka bayan kammala zaman kotun. Ta ce bayan da Gwamna Dikko Raɗɗa ya sanya hannu a dokar hukunta masu laifin aikata fyaɗe da cin zarafin bil'adama a jihar, Ma'aikatar Shari'a ta kafa kwamitin ko-ta kwana inda ba tare da ɗaukar tsawon lokaci ba kwamitin ya gano shari'a guda 50. Kwamishinar ta ƙara da cewa a yanzu haka Ma'aikatar tana da shari'a guda 40 da…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya gargaɗi sakatarorin ilimi su guji canza wurin aiki ga malamai bisa son zuciya

Gwamna Raɗɗa ya gargaɗi sakatarorin ilimi su guji canza wurin aiki ga malamai bisa son zuciya

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamna Dikko Raɗɗa ya yi wannan gargaɗin a lokacin da yake ƙaddamar da rabon kayan karatu guda 200.000 da baburan hawa guda 70 da wayoyin hannu guda ashirin ga malaman firamare gami da tallafi na kuɗi ga ɗalibai masu buƙata ta musamman. Ya bayyana cewa dole sakatarorin ilimin su cire son zuciya,ko wani dalili da ba na aiki ba wajen canzawa malaman firamare wajen aiki. Ya yi gargaɗin cewa duk sakataren ilimi da aka samu da aikata wannan aiki za a hukunta shi dai dai laifin da ya yi. Gwamnan yace shi da kanshi zai…
Read More
Nijeriya ta dawo da aƙalla mutane 390 da suka maƙale a ƙasar Nijar

Nijeriya ta dawo da aƙalla mutane 390 da suka maƙale a ƙasar Nijar

Daga USMAN KAROFI Gwamnatin Tarayya ta dawo da ‘yan Najeriya 390 da suka maƙale a Jamhuriyar Nijar, a ranar Talata, ta hannun hukumar kula da ‘yan gudun hijira, masu Ƙaura, da Waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa (NCFRMI), tare da haɗin gwiwar wasu hukumomi. An gudanar da aikin ne a makarantar horas da jami’an shige da fice (ITSK) da ke Jihar Kano, inda aka karɓi waɗanda aka dawo da su. Sun haɗa da maza manya 387, mata 2, da jariri guda. Bayan isowarsu, jami’an NCFRMI da na hukumar shige da fice (NIS) sun yi musu rijista da tantancewa domin tabbatar da…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da ɓullar cutar tsuntsaye a Kano

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da ɓullar cutar tsuntsaye a Kano

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da labarin ɓullar cutar tsuntsaye da ake kira da 'bird flu' a Jihar Kano. Cutar, wadda ta shafi nau'ukan tsuntsaye da dama da suka haɗa da kaji da agwagi da makamantansu, ta sanya al'umma cikin damuwa game da yiwuwar yaɗuwarta a shiyyar arewa. A cikin wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Dakta Taiwo Olasoju a madadin shugaban likitocin dabbobi ta ƙasa, hukumomi sun yi hasashen yiwuwar yaɗuwar cutar a yanayin sanyi da ake ciki. Shugaban ƙungiyar masu kiwon kaji ta Nijeriya (PAN) reshen jihar Kano, Dakta Usman Gwarzo, ya bayyana…
Read More
Kwana ɗaya kafin bada rahoton hauhawar farashi, har yanzu shafin Hukumar Ƙididdiga a rufe yake

Kwana ɗaya kafin bada rahoton hauhawar farashi, har yanzu shafin Hukumar Ƙididdiga a rufe yake

Daga BELLO A. BABAJI A halin yanzu al'ummar Nijeriya suna jiran tsammanin samun rahoton hauhawar farashi yayin da ya rage kwana ɗaya Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta fitar da shi, inda har yanzu shafinta na yanar gizo ya ke a rufe. Sakamakon rahoton zai bada damar yanke hukunci game da tsarin sarrafa kuɗaɗe da kewayawarsu acikin al'umma. Wa'adin fitar da bayanai game da matakin farashi na watan Disamba zai ƙare ne a ranar 15 ga watan Janairu. Mutane da dama suna ganin akwai yiwuwar NBS ta rasa damar fitar da rahoton kamar yadda ta saba game da batutuwa masu…
Read More
CAF ta ɗage gasar Africa Nations Championship zuwa Agusta 2025

CAF ta ɗage gasar Africa Nations Championship zuwa Agusta 2025

Daga USMAN KAROFI Hukumar CAF ta sanar da ɗage gasar TotalEnergies CAF African Nations Championship (CHAN) 2024 zuwa Agusta 2025. CAF ta bayyana cewa an ɗage gasar ne domin samar da ƙarin lokaci don tabbatar da cewa kayan aiki da wuraren da za a yi gasar sun kai matakin da ya dace don gudanar da gasar cikin nasara. A yayin haka, hukumar za ta gudanar da zaɓen rukunin gasar TotalEnergies CAF CHAN a Nairobi, ranar Laraba, 15 ga Janairu, 2025.
Read More
Mataimakiyar Sakatare-Janar ta MDD ta kammala ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Nijeriya

Mataimakiyar Sakatare-Janar ta MDD ta kammala ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Nijeriya

Mataimakiyar Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Amina J. Mohammed ta kammala ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Nijeriya, inda ta nemi goyon bayan tabbatar da zaman lafiya a yankin, ɗaukar matakan sauyin yanayi, da dai sauransu. Yayin da take Nijeriya, ta yi tarurruka da dama, ciki har da shugaba Bola Ahmed Tinubu, ministan Kuɗi kuma ministan tattalin arziki, Wale Edun, ministan ba da agaji, gudanar da Blbala'i da ci gaban jama'a, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda da manyan jami'an gwamnati, shugaban ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Yammacin Afrika (ECOWAS), Dr. Omar Alieu Touray da kuma tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya a ƙarƙashin…
Read More
Tinubu ya zama shugaban ƙasa na farko da ya naɗa mataimakin Darakta Janar a DSS

Tinubu ya zama shugaban ƙasa na farko da ya naɗa mataimakin Darakta Janar a DSS

Daga USMAN KAROFI Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗa Folashade Arinola Adekaiyaoja fsi+, fdc, a matsayin mataimakiyar Darakta Janar na hukumar tsaro ta DSS. Naɗin, wanda shine na farko da wani shugaban ƙasa ya yi, ya samu yabo daga ma’aikatan DSS na yanzu da wanda suka yi ritaya, waɗanda suka ce wannan mataki zai dawo da ƙwarewa a hukumar. Shugaba Tinubu ya yi wannan naɗin ne bayan shawarar darakta janar na DSS ta hannun mai ba da shawara kan tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, don inganta tsarin aikin hukumar bisa ƙa’idojin da aka kafa tun farko. Adekaiyaoja, ‘yar asalin…
Read More