14
Jan
Daga RABIU SANUSI a Kano An bayyana cewa zuwan gwamnatin Abba Kabir Yusuf ne bayan tafiyar Gwamnatin Dakta Rabiu Musa Kwankwaso Jihar Kano ta ke samun damar samar ma al'umma hanyoyin dogaro da kai. AVM Ibrahim Umaru ya bayyana haka ne a wajen ƙaddamar da shirye-shiryen da ake yi na ɗaukar matasa kimanin 6000 da za'a koyar da sana'o'i daban-daban da dogaro da kai a shiyyar Kano ta tsakkiya da ta Kudu. AVM Ibrahim Umaru Rtd wanda ya samu wakilcin mataimakin darakta na musamman na ma'aikatar kula da ayyuka na musamman a fadar gwamnatin Kano, Alhaji Habibu Madigawa. Babban daraktan…
