13
Jan
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kwamitin Raba Kuɗaɗen Asusun Tarayya (FAAC) ya raba jimillar Naira Tiriliyan 5.38 ga jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja tsakanin watan Janairu zuwa Disamba 2024. Wannan adadin ya nuna ƙarin kusan Naira Tiriliyan 1.46 fiye da Naira Tiriliyan 3.92 da Jihohi da Abuja suka samu a shekarar da ta gabata. Jihohin sun samu jimillar Naira biliyan 412.09 a watan Janairu; Naira biliyan 406.96 a watan Fabrairu; Naira biliyan 454.70 a watan Maris da kuma Naira biliyan 428.24 a watan Afrilu. Jimlar Naira biliyan 463.04 ta samu a watan Mayu; Naira biliyan 365.81 (mafi ƙarancin kasafi…
