Labarai

Layin lantarki na Benin-Omotosho katsewa ya yi, ba lalacewa ba – TCN

Layin lantarki na Benin-Omotosho katsewa ya yi, ba lalacewa ba – TCN

Daga BELLO A. BABAJI Kamfanin Raba Wutar lantarki na Ƙasa, TCN, ya ce rumbun lantarki na ƙasa bai lalace ba, kamar yadda kafafen labarai ke yaɗa wa al'umma. A ranar Asabar 11 ga watan Junairu da misalin ƙarfe 1:41 na rana ne layin Osogbo-Ihovour ya tsinke wanda ya faru ne sakamakon katsewa da na Benin-Omotosho ya yi inda ya shafi raba adadi mai yawa na wuta ga yankin Legas. Wata sanarwa da babban jami'in hulɗa da jama'a na kamfanin, Ndidi Mbah ya fitar, ta ce gabannin katsewar, megawat 4,335.63 ne adadin nauyin wutar da rumbun ya raba, yayin da ya…
Read More
Bello Turji ya yi layar zana yayin da sojoji suka kashe kwamandojin ƴan bindiga, inji NAF

Bello Turji ya yi layar zana yayin da sojoji suka kashe kwamandojin ƴan bindiga, inji NAF

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Lahadi ne Rundunar sojojin Sama ta Nijeriya (NAF), ta ce kwamandojin ƴan bindiga da dama ne suka rasa rayukansu a wani hari ta sama da jami'anta suka kai wa maɓoyarsu a Jihar Zamfara. Daraktan yaɗa labarai na NAF, Air Vice Marshal Olusola Akinboyewa ya bayyana hakan a wata sanarwa inda ya ce jami'ansu sun kai farmakin ne da haɗin-gwiwar sojojin ƙasa wanda ya raunata wasu da dama daga cikin ƴan ta'addar. Ya ce wani rahoton sirri ya tabbatar da cewa ƴan bindigar mambobin dabar sanannen jagoransu ne, Kachalla Bello Turji, waɗanda sun fuskanci mummunar…
Read More
Tinubu ya sauka a Abu Dhabi don halartar taron ci-gaban tattalin arziƙi

Tinubu ya sauka a Abu Dhabi don halartar taron ci-gaban tattalin arziƙi

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya isa birnin Abu Dhabi na ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) domin halartar tarurrukan da za a yi na Satin batutuwan Ci-gaba na Abu Dhabi (ADSW). Shugaban ƙasar UAE, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan musamman ya aika wa Shugaba Tinubu saƙon gayyatar sa zuwa taron. Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai ta kafafen sadarwa, Dada Olusegun ya bayyana hakan a kafar X inda ya ɗora wani faifan bidiyo da ke nuna yadda Tinubu ya isa ƙasar. Ya ce taken taron shi ne 'The Nexus of Next: Supercharging Sustainable…
Read More
Hukumar shari’a ta Jigawa ta kori jami’ai 3 da shawartar alƙalai 2 su yi murabus

Hukumar shari’a ta Jigawa ta kori jami’ai 3 da shawartar alƙalai 2 su yi murabus

Daga BELLO A. BABAJI A ƙoƙarinta na daƙile rashawa da ke cikin harkokin shari'a a Jigawa, Hukumar kula da Harkokin Shari'a ta jihar, ta fara ɗaukar mataki akan jami'an ɓangaren a jihar. A cikin wata takarda da Sakataren hukumar, Barista Auwalu Ɗan'azumi ya fitar, hukumar ta karɓi rahoton kwamitin bincike daga babbar kotu game da wani jami'i mai suna Iyal Ibrahim da Baffa Alhaji waɗanda aka samu da laifin sayar da wasu motocin Babbar Kotun Tarayya da ke Dutse. An yanke wa mutane biyun hukuncin kora daga aiki ƙarƙashin dokar hukumar shari'ar sashe na 41 da kuma ta jihar sashe…
Read More
Naɗa Owoade a matsayin Alafin ya saɓa wa doka – Masu zaɓen sarki ga Gwamnan Oyo

Naɗa Owoade a matsayin Alafin ya saɓa wa doka – Masu zaɓen sarki ga Gwamnan Oyo

Daga BELLO A. BABAJI Amincewa da naɗin Frins Abimbola Owoade a matsayin sabon Alafin ɗin Oyo ya fusata masu zaɓen sarki da Gwamna Seyi Makinde na jihar ya yi a Masarauta mai daɗaɗɗiyar tarihi ta Oyomesi. A wata sanarwa da Kwamishinan yaɗa Labarai da Wayar da kai na jihar, Frins Dotun Oyelade ya fitar, gwamnan ya amince da naɗa Owoade a matsayin Alafin ɗin bayan nazari da gabatar da shi da Oyomesi suka yi. Haka ma Kwamishinan harkokin ƙananan hukumomi da masarautu, Hon Ademola Ojo ya ce sanarwar ta rufe duk wasu batutuwa na al'umma ko ƙa'idodin shari'a da aka…
Read More
Satar Diezani: Gwamnatin Amurka ta dawo wa Nijeriya da Dala 52.88m

Satar Diezani: Gwamnatin Amurka ta dawo wa Nijeriya da Dala 52.88m

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Juma'a ne Gwamnatin Amurka ta mayar wa Nijeriya Dala miliyan 52.88 da aka alaƙanta su da tsohuwar ministar man fetur, Diezani Madueke. An gano kuɗaɗen ne na wasu kadarori da aka danganta su da tsohuwar ministar da waɗanda suke tare da ita. Jakadan Amurka, Richard M. Mills da wasu jami'an gwamnatin Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Antoni-Janar na ƙasa, Lateef Fagbemi suka kammala yarjejeniyar a Ma'aikatar Shari'a a Abuja. An gudanar da yarjejeniyar ne kan amfani da kuɗaɗen wajen yin ayyukan da suka dace don amfanin Nijeriya da al'ummarta. Haka kuma Bankin Duniya zai sanya ido…
Read More
Gwamnatin Kano ta bai wa ɗan bijilantin da ƴan daba suka raunata tallafin N500,000

Gwamnatin Kano ta bai wa ɗan bijilantin da ƴan daba suka raunata tallafin N500,000

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamnatin Jihar Kano ta tallafa wa matashi Musa Muhammad Kallah dake aikin bijilanti da ƴan daba suka farmaka da kuɗi har naira dubu dari biyar don cigaba da kula da lafiyarsa. Da ya ke miƙa kuɗin, wakilin Gwamna Abba Kabir Yusuf, Babban daraktan ayyuka na musamman kuma mai kula da ɓangaren harkokin jami'an tsaro AVM Ibrahim Umaru (RTD) ya bayyana irin halin da mai girma gwamna ya tsinci kansa yayin da labarin ya same shi. Babban Daraktan ya ce ƙoƙarin mai girma gwamna ne na tausaya tare da nuna damuwa ga dukkan wani mutum da…
Read More
Remi Tinubu ta miƙa ta’aziyya ga gwamnan Jigawa bisa rashe-rashen da aka yi masa

Remi Tinubu ta miƙa ta’aziyya ga gwamnan Jigawa bisa rashe-rashen da aka yi masa

Daga UMAR AKILU MAJERI Dutse Uwar gidan shugaban ƙasar Nijeriya Olu Remi Tinubu ta jajantawa Gwamna Umar Namadi Bisa rashin mahaifiyarsa Hajiya Maryam A Namadi da babban ɗansa Abdulwahab Umar Namadi da suka rasu a kwanan baya. Remi ta ziyarci fadar gwamnatin Jihar ne a ranar Asabar tare da tawagarta daga fadar shugaban ƙasa cikin wani yanayi da yake nuna alhini da damuwa a fuskarta bisa rashin da a ka yiwa gwamnan jihar ta Jigawa da al,ummar Jihar baki ɗaya a kwanan baya . Remi a cikin bayananta tace dukkan mai rai mamaci ne kuma kowa ita yake jira wato…
Read More
Kotu ta kori ƙarar da tsagin Mustapha Inuwa na PDP ya shigar akan takwarorinsa na Katsina

Kotu ta kori ƙarar da tsagin Mustapha Inuwa na PDP ya shigar akan takwarorinsa na Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Wata Babban Kotu a Katsina ta kori ƙarar da ɓangaren Mustapha Inuwa na jam'iyyar PDP ya shigar inda take ƙalubalantar uwar jami'yyar na jiha da zaɓen shugaban jam'iyyar a matakin kananan hukumomi. Da ya ke hukunci game da ƙarar, Mai Shari'a Abbas Bawale ya ce kotu ba ta da hurumin shiga harkokin cikin gida na jami'yya. Ya bada misali da hukuncin Kotun Ƙoli da na Kotun Ɗaukaka ƙara duk akan irin wannan ƙara inda kotunan suka yanke ire-iren waɗannan hukuncin. Mai Shari'a Bawale ya ƙara da cewa hakan ma biyayya ce ga manyan kotuna saboda…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da koyon karatun fasahar AI kyauta ga matasa

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da koyon karatun fasahar AI kyauta ga matasa

Daga BELLO A. BABAJI A ƙoƙarinta na samar wa matasa ilimin fasahar zamani, Ma'aikatar Ƙirƙira da Kimiyya da Fasaha tare da haɗin-gwiwa da Sakatariyar Baitul Mali ta Commonwealth da Hukumar sadarwa ta Intel, ta ƙaddamar da makarantar koyon fasahar inganta harkokin komfuta ga matasa. Ma'aikatar ta ce ilimin, wanda aka yi wa laƙabi da Artificial Intelligence (AI), zai bai wa matasan damar koyon karatun muhimman darussa da suka shafi fasahar AI, ƙa'idodin aiki, kayayyakin aiki da kuma yadda ake amfani da su a ko'ina a Duniya. Haka kuma zai ba su damar zama wakilai game da fasahar da gudanar da…
Read More