Satar Diezani: Gwamnatin Amurka ta dawo wa Nijeriya da Dala 52.88m

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Juma’a ne Gwamnatin Amurka ta mayar wa Nijeriya Dala miliyan 52.88 da aka alaƙanta su da tsohuwar ministar man fetur, Diezani Madueke.

An gano kuɗaɗen ne na wasu kadarori da aka danganta su da tsohuwar ministar da waɗanda suke tare da ita.

Jakadan Amurka, Richard M. Mills da wasu jami’an gwamnatin Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Antoni-Janar na ƙasa, Lateef Fagbemi suka kammala yarjejeniyar a Ma’aikatar Shari’a a Abuja.

An gudanar da yarjejeniyar ne kan amfani da kuɗaɗen wajen yin ayyukan da suka dace don amfanin Nijeriya da al’ummarta.

Haka kuma Bankin Duniya zai sanya ido wajen tabbatar da an yi abin ya kamata da kuma kiyaye ƙa’idodin yaƙi da rashawa a mataki na Ƙasa-da-ƙasa.