Labarai

‘Yan bindiga sun kai hari asibiti, sun harbe likita da sace ma’aikata a Katsina

‘Yan bindiga sun kai hari asibiti, sun harbe likita da sace ma’aikata a Katsina

‘Yan bindiga sun kai hari babban asibitin da ke ƙaramar hukumar Ƙankara a Jihar Katsina, inda suka harbi wani likita tare da yin garkuwa da wasu ma’aikatan asibitin da ba a san adadinsu ba. Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:00 na yammacin ranar Talata, inda suka harbi Dr. Murtala Sale Dandashire a ƙafa. Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun shiga harabar asibitin cikin tsari, suna ta harbe-harbe, wanda ya jefa ma’aikata da marasa lafiya cikin firgici. An tabbatar da cewa Dr. Dandashire, wanda aka harba a ƙafarsa, yana raye…
Read More
Zan iya taimakon gwamnatin Tinubu wajen shawo matsalolin tattalin arziki, amma ba zan yi ba – Sarki Sunusi

Zan iya taimakon gwamnatin Tinubu wajen shawo matsalolin tattalin arziki, amma ba zan yi ba – Sarki Sunusi

Daga USMAN KAROFI Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce ba zai bayar da shawara ga gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan yadda za a magance matsalolin tattalin arzikin ƙasar ba. Sanusi ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin gabatar da jawabinsa a taron tunawa da marigayi Cif Gani Fawehinmi karo na 21, da aka gudanar a Legas. Yayin da yake jagorantar taron, Sanusi ya ce ya fara taimaka wa gwamnati a baya amma yanzu ya yanke shawarar daina yin hakan. A cewarsa: “Zan iya bayar da wasu mahimman bayanai kan abin da muke fuskanta da yadda…
Read More
Kare kasafin 2025: Ministan Kuɗi ya nemi a yi ganawar sirri game da tallafin fetur

Kare kasafin 2025: Ministan Kuɗi ya nemi a yi ganawar sirri game da tallafin fetur

Daga BELLO A. BABAJI Ministan Kuɗi kuma Kodineta Minista na Tattali, Wale Edun, wanda sanatoci suka dabaibaye shi da tambayoyi a lokacin kare kasafi, ya buƙaci kwamitin tantancewa da ya samar da keɓantaccen waje don bada amsoshinsu. Hakan na zuwa ne a lokacin da Ministan ya tsaya a gaban kwamitin don kare matakin aiwatar da kasafin kuɗin ma'aikatarsa na shekarar 2024. A lokacin da Sanata Abdul Ningi daga Bauchi ta Tsakiya (PDP), ya buƙaci Ministan ya yi bayani game da yadda aka sarrafa kuɗaɗen tallafin fetur a shekarar 2024, sai Minista Edun ya ce a ba shi damar amsa tambayar…
Read More
JAMB ta fidda ƙa’idojin yin rajista a 2025

JAMB ta fidda ƙa’idojin yin rajista a 2025

Daga USMAN KAROFI A wata sanarwa da aka wallafa a shafinta na X a ranar Laraba, JAMB ta tabbatar wa da masu neman shiga jarabawar cewa za a sanar da cikakkun bayanai kan tsarin rijistar nan ba da jimawa ba. Sanarwar ta ce: “A lura masu neman gurbin jarabawar UTME/DE na 2025! Rijista ba a fara ba tukuna. Duk da haka, za mu sanar da cikakkun bayanai nan gaba. Kuna iya samun NIN da kuma lambar waya wacce ba a taɓa amfani da ita wajen rijista ba don ƙirƙirar lambar ku ta profile kafin lokacin.” Haka kuma, JAMB ta bayyana…
Read More
Ranar ‘Yan Mazan Jiya: Shettima da wasu manyan jami’an gwamnati sun jinjina wa sojojin da suka kwanta-dama

Ranar ‘Yan Mazan Jiya: Shettima da wasu manyan jami’an gwamnati sun jinjina wa sojojin da suka kwanta-dama

Daga BELLO A. BABAJI Yayin da ake bikin tunawa da sojojin da suka rasa rayukansu a bakin aiki, manyan jami'an gwamnati da dama ne suka halarci taron a filin taro na Eagles Square dake Abuja, a ranar 15 ga watan Junairu. Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Bola Tinubu, shi ne wanda ya jagoranci sauran manyan jami'an gwamnati don sara wa sojojin da iyalansu bisa namijin ƙoƙarin da suka yi wajen bai wa Nijeriya da al'ummarta tsaro. Cikin waɗanda suka halarci taron akwai shugabancin Majalisun Dattawa da Wakilai, shugabannin sojoji, Sufeton ƴan sanda da kuma Alƙalin Alƙalan…
Read More
Rundunar soja ta haramta ayyukan jirgi marar matuƙi a Borno

Rundunar soja ta haramta ayyukan jirgi marar matuƙi a Borno

Daga USMAN KAROFI Rundunar haɗin kai ta sojojin Nijeriya da ke Arewa maso Gabas ta haramta amfani da jirage marasa maƙuka (drones) a yankin. Air Commodore U. U. Idris, kwamandan rundunar ta sama, ya bayyana hakan a wata sanarwa, yana mai cewa amfani da jiragen ba tare da izini ba na barazana ga tsaro a jihohin Borno, Yobe da Adamawa. Sanarwar ta nuna damuwa kan yadda hukumomin gwamnati da masu zaman kansu ke amfani da jirgi marar matuƙi ba tare da bin ƙa’idojin da suka dace ba. Kwamandan ya ce an sha samun rahotannin ganin jiragen da kuma amfani da…
Read More
Za mu cigaba da samar wa matasa aikin ɗamara don taimaka wa tsaro – Hon. Rurum

Za mu cigaba da samar wa matasa aikin ɗamara don taimaka wa tsaro – Hon. Rurum

Daga RABI'U SANUSI Wakilin Ƙananan Hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure a Majalisar Wakilai, RT Hon. Kabiru Alhassan Rurum ya bayyana cewa zai cigaba da samo guraben aiki ga matasan yankunan ƙananan hukumominsa a matakin Tarayya musamman a ɓangarorin aikin tsaro. Rurum Wanda shine Shugaban Kwamitin Kula da harkokin Sojin sama na Majalisar ya bayyana hakan a wajen taron yaye sabbin dakarun Sojin sama da suka kammala karɓar horo a garin Kaduna. Ɗan majalisar ya ce cigaba da ƙarfafa wa matasa gwiwa da tallafa musu samun aikin zai ƙara inganta sha'anin tsaro dake fuskantar ƙalubale a kasarnan. Ya ce a wannan…
Read More
Jami’an tsaro sun sake kama Mahdi Shehu

Jami’an tsaro sun sake kama Mahdi Shehu

Daga USMAN KAROFI An samu rahoton cewa jami’an tsaro da ake zargin na DSS ne, sun kama fitaccen mai fafutukar siyasa, Mahdi Shehu. An ce an ɗauke shi ne a asibitin sa da ke Unguwar Dosa, Kaduna, misalin ƙarfe 11:00 na safe, ta hannun jami’ai sanye da kayan fararen hula. Har yanzu babu wata sanarwa daga hukumomin tsaro game da kamen. Sai dai, Buhari Mahdi, ɗansa, ya tabbatar da cewa ba su samu wata alaƙa da shi ba tun bayan da aka ɗauke shi. A watan Disamban 2024, Mahdi Shehu ya taɓa fuskantar kame tare da gurfanarwa a gaban kotu…
Read More
Majalisar Dattijawa ta jinjina wa Ministan Labarai da nema wa ma’aikatarsa kason kasafi na musamman

Majalisar Dattijawa ta jinjina wa Ministan Labarai da nema wa ma’aikatarsa kason kasafi na musamman

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Talata ne Majalisar Dattijawa ta yaba wa Ministan Labarai da Wayar kai, Alhaji Idris Mohammed bisa namijin ƙoƙarinsa wajen gudanar da harkokin labarai da suka shafi tsare-tsare da shirye-shiryen gwamnati. Mambobin kwamitin labarai na majalisar suka bada shaidar a lokacin da Ministan ya tsaya a gaban kwamitin don kare kasafin ma'aikatarsa na 2025. Sanatocin kwamitin sun koka kan yadda aka samo kaso mara tsoka na kasafin ga ma'aikatar wanda suke ganin ba zai wadaci ayyukanta ba. Don haka ne kwamitin ya yanke shawarar tsoma baki game da lamarin saboda bai wa Ma'aikatar damar cigaba…
Read More