Labarai

Gidauniyar Muktariyya ta yi bikin yaye ɗalibai a Kano

Gidauniyar Muktariyya ta yi bikin yaye ɗalibai a Kano

Daga HARUNA AKARAɗA a Kano Gidauniyar Mukhtariyya ta gudanar da bikin yaye ɗalibai karo na biyar a Jihar Kano. Jigo a Jam'iyyar APC ta Jihar Kano, Hon Dr. Mukhtar Ishaƙ Yakasai (Jagora), kuma shugaban cibiyar gidauniyar Mukhtariyya, shine yake ɗaukar nauyin karatun ɗaliban kyauta, domin cigaba tallafawa mara ƙarfi da marayu a Jihar Kano. Wannan taro ya samu  halartar manyan baƙi na jam'iyyar APC dake Jihar Kano kamar su tsohon kwamishinan ilimi, Hon. Sanusi Sa'id Kiru, tsohowar kwamishiniyar mata, Malama Dr. Zahara'u, tsohon kwamishinan addini, Dr. Muhammad Nafizi Bichi, Hon, Ahmad S Aruwa, S A.Alhaji Tijjani Mailafiya Sanka, Shugaban gamayyar…
Read More
An buƙaci Fulani su zama masu haɗin kai da neman zaman lafiya a Legas

An buƙaci Fulani su zama masu haɗin kai da neman zaman lafiya a Legas

Daga BALA KUKKURU a Legas Sarkin Fulanin ƙaramar Hukumar Badagiry da ke Jihar Legas, Alhaji Umar Mohammed Bello, ya buƙaci al'ummar Fulanin yankin Badagiri da kewayenta gabaɗaya da su zama masu haɗin kai da junansu tare da neman zaman lafiya a garin na Badagiry da kewayenta bakiɗaya. Sarkin Fulanin, wanda ya kasance ɗan asalin jihar Neja da ke yankin arewacin Nijeriya, mazaunin garin Badagiri ta Jihar legas, ya buƙaci hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata a lokacin da yake gabatar da jawabinsa na taron bikin wankan sarautarsa ta sarkin Fulanin Badagiry da kewayenta gabaɗaya. Taron bikin wankan sarautar…
Read More
Miyetti Allah Mokwa ta nemi yayanta su nemi wajen zama na dindindin 

Miyetti Allah Mokwa ta nemi yayanta su nemi wajen zama na dindindin 

Daga JAMEEL GULMA a Kebbi  Sakataren ƙungiyar Miyetti Allah kuma mataimaki na musamman ga Mataimakin Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Bello S. Fulani, ya nemi al’ummar Fulani makiyaya da ke zaune a yankin ƙaramar hukumar Mokwa a Jihar Neja su nemi wuraren zama na dindindin, don cin moriyar dimukraɗiyya. Ya yi wannan kiran ne a ofishinsa da ke garin Mokwa ranar Talatar da ta gabata. Bello Fulani ya bayyana cewa, wannan gwamnatin ta Jihar Neja a ƙarƙashin jagorancin Umar Bago a shirye ta ke ta samar da ilmi ga Fulani makiyaya a rugarsu. Saboda haka a maimakon yau suna nan gobe…
Read More
Gwamnatin Tinubu ba ta buƙatar Sanusi ya tallata ta – Idris

Gwamnatin Tinubu ba ta buƙatar Sanusi ya tallata ta – Idris

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamnatin Tarayya ta yi wa Sarki Muhammadu Sanusi II raddi tana mai cewa, duk da ba ya tare da ita, akwai buƙatar ya ajiye son rai da nuna ɓangaranci ya mayar da hankali kan buƙatun ’yan Nijeriya, tana mai cewa, Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba ta buƙatar sai sarkin ya tallata kyawawan manufofinta kafin ta karɓu. Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa, a yayin wani taron tunawa da fitaccen lauyan nan ɗan gwagwarmaya, Cif Gani Fawehinmi, da ya gudana a ranar Laraba a Jihar Legas, Sarkin Kano na 16 ya furta kalaman cewa, yana da…
Read More
Gwamnoni sun goyi bayan yin kwaskwarima ga ƙudirin harajin Tinubu

Gwamnoni sun goyi bayan yin kwaskwarima ga ƙudirin harajin Tinubu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD A ƙarshe, ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya ta amince da ƙudirin sake fasalin harajin da ake shirin yi a Majalisar Dokokin ƙasar, amma sun gabatar da sabuwar hanyar rabon harajin ɓAT. Hakan na ƙunshe cikin sanarwar da ƙungiyar gwamnonin ta fitar a ranar Alhamis, wadda ta samu sa hannun shugabanta kuma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaƙ. Gwamnonin sun kuma fitar da sabon tsari na rabon haraji a Nijeriya, bayan wata ganawa da suka yi da kwamitin da aka kafa domin nazari kan ƙudurin sabuwar dokar harajin. Ana iya tuna cewa, a ƙarshen shekarar da ta gabata ce Shugaba…
Read More
Kotu ta wanke wanda ya yi barazanar kawo IPOB Legas

Kotu ta wanke wanda ya yi barazanar kawo IPOB Legas

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wata babbar kotun jihar Legas da ke zama a dandalin Tafawa Balewa ta sallami wani shugaban ƙabilar Ibo, Frederick Nwajagu, tare da wanke shi daga tuhumar ta’addanci. A ranar 5 ga Afrilu, 2023, wata Kotun Majistare ta Jihar Legas da ke Yaba ta bayar da umarnin a tsare Nwajagu a gidan yari na Ikoyi, yayin da babbar kotun Jihar Legas ta ƙi bayar da belinsa daga baya. An zargi Nwajagu da yin barazanar gayyatar ‘yan ƙungiyar ta'addancin Biyafara ta IPOB zuwa Legas domin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙabilar Ibo idan har gwamnatin tarayya ta kasa…
Read More
Jigon APC a Zamfara ya bada kyautar motoci ga ‘yan jam’iyyar APC

Jigon APC a Zamfara ya bada kyautar motoci ga ‘yan jam’iyyar APC

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Wani jigon jam’iyyar APC a Jihar Zamfara, Alhaji Yazid Shehu Ɗanfulani ya bayar da kyautar motoci na alfarma guda 20 ga shugabannin jam’iyyar da magoya bayan jam’iyyar a jihar ta Zamfara. Ɗanfulani wanda shi ne tsohon kwamishinan kasuwanci da masana’antu na jihar ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da motocin ga waɗanda suka ci gajiyar motocin a Gusau yau Alhamis. A cewar sa, wannan karimcin na da nufin tallafa wa shugabannin jam’iyyar da magoya bayan ta domin ganin sun himmatu wajen ciyar da jam’iyyar gaba a jihar. “Wannan ita ce gudunmawata ga wasu…
Read More
Gwamnan Zamfara ya amince da ɗaukar malamai 2,000 aiki a jihar

Gwamnan Zamfara ya amince da ɗaukar malamai 2,000 aiki a jihar

Daga BELLO A. BABAJI A ƙoƙarinsa na inganta harkar ilimi, Gwamna Dauda Lawal na Zamfara ya amince da a ɗauki malamai guda 2,000 aiki a makarantun faɗin jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin zaman Majalisar Zartarwa ƙarƙashin jagorancinsa a gidan gwamnatin jihar dake Gusau. A wata sanarwa da Kakakinsa, Sulaiman Bala Idris ya fitar, gwamnan ya jaddada shirin ɗaukar malamai aiki a matsayin ɗaya daga cikin alƙawuran da ya yi a lokacin yawon neman zaɓe. Sanarwar ta bayyana cewa, ilimi shi ne abu na biyu da gwamnatin Dauda Lawal ya mayar da hankali a kai wanda a halin…
Read More
Gwamnatin Kano ta haɗa hannu da bankin Musulunci don gina makarantun Turanci da Larabci

Gwamnatin Kano ta haɗa hannu da bankin Musulunci don gina makarantun Turanci da Larabci

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin, Abba Kabir Yusuf, ta sanar da shirinta na haɗin-gwiwa da Bankin Musulunci (IDB) don samar da makarantu guda huɗu da za riƙa amfani da yarukan Turanci da Larabci wajen karantar da ɗalibai. A cikin wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Kakakinsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, gwamnan ya ce gwamantin ta yanke hakan ne a ƙoƙarinta na bai wa yara almajirai damar koyon karatun zamani tare da rage adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar. Gwamna Abba Kabir ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke ƙaddamar…
Read More
Ɗan jarida Lawal Sa’idu Funtua ya rasu a Katsina

Ɗan jarida Lawal Sa’idu Funtua ya rasu a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Lawal Sa'idu tsohon ɗan jarida kuma wakilin jaridar Peoples Daily a Katsina ya rasu. Ya rasu da safiyar Alhamis bayan fama da dogon rashin lafiya a Katsina. Marigayi Lawal Sa'idu ya yi aiki a gidan rediyon Katsina, gidan Talbijin na DITV Kaduna, tsohuwar jaridar Today da Peoples Daily. Ya kuma riƙe muƙamin shugaban ƙungiyar 'yan jarida reshen kafofin yaɗa labarai (Correspondants chapel) har karo na biyu a Katsina. Marigayi Lawal Sa'idu ya bar mata biyu da ya'ya da dama.
Read More