Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wata babbar kotun jihar Legas da ke zama a dandalin Tafawa Balewa ta sallami wani shugaban ƙabilar Ibo, Frederick Nwajagu, tare da wanke shi daga tuhumar ta’addanci.
A ranar 5 ga Afrilu, 2023, wata Kotun Majistare ta Jihar Legas da ke Yaba ta bayar da umarnin a tsare Nwajagu a gidan yari na Ikoyi, yayin da babbar kotun Jihar Legas ta ƙi bayar da belinsa daga baya.
An zargi Nwajagu da yin barazanar gayyatar ‘yan ƙungiyar ta’addancin Biyafara ta IPOB zuwa Legas domin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙabilar Ibo idan har gwamnatin tarayya ta kasa kare su daga hare-hare.
Sai dai kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin watanni 12 a gidan yari, bayan da aka kama shi da laifin nuna kansa a matsayin shugaban IPOB a jihar Legas, wanda ya saɓa wa dokar Oba da sarakunan jihar Legas.
Nwajagu wanda ke shari’a a gaban mai shari’a Yetunde Adesanya ta babbar kotun jihar Legas tun daga shekarar 2023, bisa tuhume-tuhume 9 da suka haɗa da yunƙurin aikata ta’addanci, ɗaukƙr nauyin ta’addanci, shiga ayyukan ta’addanci da kuma taron tallafa wa haramtacciyar ƙungiyar ta’addanci, an sallame shi tare da wanke shi a ranar Laraba, 15 ga Janairu, 2025.
A cewar jaridar Sahara Reporters, ɗaya daga cikin lauyoyin Nwajagu, Barista Fabian Onwughalu, shugaban ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo, reshen Legas, a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, ya ce tawagar masu kare za shi yi aiki don tabbatar da hukuncin.
