Jigon APC a Zamfara ya bada kyautar motoci ga ‘yan jam’iyyar APC

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Wani jigon jam’iyyar APC a Jihar Zamfara, Alhaji Yazid Shehu Ɗanfulani ya bayar da kyautar motoci na alfarma guda 20 ga shugabannin jam’iyyar da magoya bayan jam’iyyar a jihar ta Zamfara.

Ɗanfulani wanda shi ne tsohon kwamishinan kasuwanci da masana’antu na jihar ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da motocin ga waɗanda suka ci gajiyar motocin a Gusau yau Alhamis.

A cewar sa, wannan karimcin na da nufin tallafa wa shugabannin jam’iyyar da magoya bayan ta domin ganin sun himmatu wajen ciyar da jam’iyyar gaba a jihar.

“Wannan ita ce gudunmawata ga wasu ’ya’yan jam’iyyarmu da suke aiki ba dare ba rana domin ci gaban babbar jam’iyyarmu,” inji shi.

Ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da marawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ƙaramin ministan tsaro, Hon. Bello Muhammed Matawalle a ƙoƙarin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar ta Arewa maso Yamma da Najeriya baki ɗaya.

Ɗanfulani ya yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar APC a jihar da su ci gaba da haɗa kan su, kuma su ci gaba da jajircewa wajen gina jam’iyyar a jihar.

“A matsayinmu na ’yan ƙasa nagari da ’yan jam’iyya, dole ne mu kiyaye haɗin kai, zaman lafiya da kwanciyar hankali domin ci gaban jam’iyyar a jihar,” in ji shi.

Da yake mayar da martani shugaban jam’iyyar APC na jiha Alhaji Tukur Umar Ɗanfulani ya yabawa Hon. Yazid Ɗanfulani bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban jam’iyyar APC a jihar.

Ɗanfulani wanda ya samu wakilcin sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar na jiha, Malam Yusuf Idris ya ce waɗanda suka ci gajiyar tallafin sun haɗa da, Ibrahim Ɗanmalikin Gidan Goga, mai baiwa ƙaramin ministan tsaro shawara na musamman kan harkokin siyasa, Hon. Bello Muhammad Matawalle wanda ya karɓi sabuwar mota ƙirar High Lander Jeep.

Sauran waɗanda suka ci gajiyar tallafin sun haɗa da tsohon kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Hon. Ibrahim Magaji Dosara wanda ya karɓi sabuwar mota ƙirar Mercedes Benz. Hon Murtala Garba, wanda ya ƙarɓi Peogeout 307, Alhaji Mande Aluta (Shugaban ƙungiyar sulhu ta APC reshen jihar Zamfara) ya karɓi mota ƙirar Mercedes Benz da Murtala STV shima ya karɓi Peogeout 307.

Ya yi nuni da cewa, sauran motoci 15 da za a miƙa wa sauran waɗanda suka amfana daga cikin magoya bayan jam’iyyar a faɗin jihar.

Ya yi kira ga ofishin siyasa a ƙarƙashin jam’iyyar APC da su yi koyi da Yazid Ɗanfulani kan goyon baya da ƙarfafa gwiwar shugabannin jam’iyyar da magoya bayansa a faɗin jihar.

“Wannan abin farin ciki ne, samun jiga-jigan jam’iyya irin su Yazid Ɗanfulani manuniya ce cewa APC ta ci gaba da zama jam’iyyar siyasa mafi ƙarfi a Zamfara.

“A madadin shugabannin jam’iyyar, muna godiya da irin wannan karimcin. Wannan alama ce da ke nuna cewa jam’iyyar APC na da gagarumar nasara ga zaɓukan da za a yi a jihar nan gaba,” in ji Shugaban Jam’iyyar.

Da yake mayar da martani a madadin waɗanda suka ci gajiyar shirin, ƙungiyar SA ta fuskar siyasa ga Hon. Minista, Ibrahim Ɗanmalikin Gidan Goga ya tabbatarwa Danfulani bisa wannan karamcin da ya nuna musu.

“Muna ɗaukar wannan a matsayin abin ƙwarin guiwa, za mu ci gaba da gudanar da ayyukan ci gaba, ci gaban jam’iyyar a jihar.” a cewar Ɗan Maliki.