17
Jan
Daga BELLO A. BABAJI Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) ta yi tir da kisan kiyashin da aka yi wa fararen hula a yankin Kukawa na Jihar Borno dake Arewa maso Gabashin Nijeriya. A wata sanarwa da Kodinetan Jin-ƙai na Majalisar a Nijeriya, Mohamed Malick ya fitar, MƊD ta bayyana kisan mutane 40 da wasu haramtattun mayaƙa suka yi a garin Dumba a ranar 12 ga watan Junairu a matsayin abin tashin hankali. Mayaƙan sun kashe mutanen ne waɗanda galibin su manoma da masunta ne bayan zargin su da taka dokarsu ta hana gudanar da harkokin gona a yankin. Malick ya jajanta…
