Daga USMAN KAROFI
An samu rahoton cewa jami’an tsaro da ake zargin na DSS ne, sun kama fitaccen mai fafutukar siyasa, Mahdi Shehu. An ce an ɗauke shi ne a asibitin sa da ke Unguwar Dosa, Kaduna, misalin ƙarfe 11:00 na safe, ta hannun jami’ai sanye da kayan fararen hula. Har yanzu babu wata sanarwa daga hukumomin tsaro game da kamen. Sai dai, Buhari Mahdi, ɗansa, ya tabbatar da cewa ba su samu wata alaƙa da shi ba tun bayan da aka ɗauke shi.
A watan Disamban 2024, Mahdi Shehu ya taɓa fuskantar kame tare da gurfanarwa a gaban kotu bisa yaɗa wani bidiyo da aka ce ya saba da gaskiya a dandalin sada zumunta.
Daga bisani, kotun babban Jihar Kaduna ta ba shi beli a ranar 9 ga Janairu, 2025, inda aka sanya kuɗin beli Naira miliyan uku tare da neman manyan malamai biyu su tsaya masa.
A makon da ya gabata, Shehu ya yi jerin saƙonni a shafukansa na sada zumunta inda ya gode wa masu goyon bayansa yayin da yake fuskantar wannan lamari. Ya ce addu’o’in su sun taimaka masa, tare da gode wa masu suka da masu zaman shiru. Wannan lamari ya ƙara janyo hankulan jama’a kan matsayinsa a harkokin siyasa da fafutuka.