Majalisar Dattijawa ta jinjina wa Ministan Labarai da nema wa ma’aikatarsa kason kasafi na musamman

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Talata ne Majalisar Dattijawa ta yaba wa Ministan Labarai da Wayar kai, Alhaji Idris Mohammed bisa namijin ƙoƙarinsa wajen gudanar da harkokin labarai da suka shafi tsare-tsare da shirye-shiryen gwamnati.

Mambobin kwamitin labarai na majalisar suka bada shaidar a lokacin da Ministan ya tsaya a gaban kwamitin don kare kasafin ma’aikatarsa na 2025.

Sanatocin kwamitin sun koka kan yadda aka samo kaso mara tsoka na kasafin ga ma’aikatar wanda suke ganin ba zai wadaci ayyukanta ba.

Don haka ne kwamitin ya yanke shawarar tsoma baki game da lamarin saboda bai wa Ma’aikatar damar cigaba da sauke nauyin ayyukan da suka rataya a wuyanta.

Kwamitin ya kuma ƙi amincewa da kasafin kuɗin ganin yadda ba zai iya wadatar da ita ba a yayin harkokinta.

A lokacin da ta ke jinjina wa ministan, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan (PDP-Kogi), ta shawarci Ministan da ya faɗaɗa ayyukansa na wayar da kan ƴan ƙasa game da darajarsu wajen mayar da hankali akan matasa, ta na mai cewa ma’aikatar tana da buƙatar isassun kuɗaɗe don cimma hakan.