Labarai

Majalisar Zartarwa ta kira taron gaggawa domin tattauna batun zanga-zanga da ake shirin yi

Majalisar Zartarwa ta kira taron gaggawa domin tattauna batun zanga-zanga da ake shirin yi

Bayanai sun fara bayyana cewa majalisar zartaswa ta yi wani taron gaggawa a kan shirin zanga-zanga da ake yi. Ministan yaɗa labarai, Muhammed Idris shine ya bayyana haka a ranar Laraba, a Abuja. Ya ce, gwamnati har yanzu ba ta bar yin aikinta ba. Don haka, za ta yi duk abinda ya dace domin ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasa. Kamar yadda kuke gani, mun zo ne mu tattauna batutuwa da suka shafi ƙasa. Domin muhimmanci lamarin ku na gani a ofishin sakataren gwamnatin Tarayya a ke wannan taron. Dukkan mu muna aiki yadda Nijeriya za…
Read More

Ajaero ya bayyana matsayar NLC kan zanga-zangar tsadar rayuwa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), ta musanta batun cewa ta janye daga zanga-zangar tsadar rayuwa da ake shirin yi faɗin Nijeriya, ta na mai cewa ba ta ɗaya daga cikin waɗanda su ka shirya ta. Shugaban ƙungiyar, Joe Ajaero ya bayyana haka cikin wata takarda da ƙungiyar ta fitar a ranar Talata, inda ya ce ba za su janye daga zanga-zangar da ba su suka tada batunta ba. Ya ce ƙungiyar tana da tsarinta na cikin gida game da yin hukunci kan ababan da su ka shafi al'umma cikin har da zanga-zanga. Ya ƙara da cewa…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta bada tallafin tiriliyan ɗaya ga masana’antu

Gwamnatin Tarayya ta bada tallafin tiriliyan ɗaya ga masana’antu

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da ba da tallafin Tiriliyan ɗaya ga masana'antu cikin shekara ɗaya. Shugaban hukumar FIRS, Zacch Adedeji shine ya sanar da hakan lokacin da ya ke faɗin akwai wani tallafin shima domin ya inganta harkar masana'antu a faɗin ƙasar. Ministan kuɗi da shugaban hukumar FIRS sune suka bayyana haka lokacin wata tattaunawa da su ka yi a kan ƙudurin kuɗi na 2024, wanda Sanata Sani Musa ya jagoranta.
Read More
Lokpobiri ya sasanta Ɗangote da NNPC

Lokpobiri ya sasanta Ɗangote da NNPC

Sanata Heineken Lokpobiri, ƙaramin Ministan Man Fetur ya kira wani babban taro na masu ruwa da tsaki a harkar man fetur da iskar gas domin warware matsalolin da suka taso tsakanin Ɗangote da Gwamnatin Tarayya. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Nneamaka Okafor, mai baiwa ministan shawara ta musamman kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa ta fitar. Taron wanda aka gudanar a ranar Litinin a Abuja ya samu halartar Alhaji Aliko Ɗangote, Mista Farouk Ahmed, Shugaban Hukumar,NMDPRA. Sauran sun haɗa da Mista Gbenga Komolafe, Shugaban Hukumar, NUPRC da Malam Mele Kyari, Babban Jami’in Rukunin Kamfanin Man Fetur…
Read More
Tsadar rayuwa: Mun janye daga zanga-zangar da muka ƙirƙiro – Murtala Gamji

Tsadar rayuwa: Mun janye daga zanga-zangar da muka ƙirƙiro – Murtala Gamji

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Shugaban Majalisar Matasa na Nijeriya, Kwamared Murtala Muhammed Garba wanda aka fi sani da Murtala Gamji, wato jigon da ya yi tunanin ƙirƙiro da zanga-zangar da ake shirin yi ƙarshen wannan watan nan akan tsadar rayuwar da al'ummar ƙasar ke fama da ita ya ankarar da al'umma wata mummunar manufa da wasu mutanen Kudancin ƙasar ke da shi akan zanga-zangar. Gamji ya ce sun ƙirƙiro da zanga-zangar ne domin kira ga gwamnati ga alhalin da 'yan ƙasa ke ci akan tsadar rayuwa, harkar tsaro da sauran matsaloli da suka yi wa Nijeriya katutu,…
Read More

Shugaban ƙasar Gabon ya gayyaci Ɗangote don sanya hannun jari a siminti da taki

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Shugaba Brice Oligui Nguema na ƙasar Gabon ya gayyato shugaban kamfanin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote zuwa ƙasarsa domin ƙulla harkar kasuwanci a ɓangarorin siminti da taki musamman domin haɓaka harkar noma. A lokacin ziyarar, Ɗangote ya gana da Shugaba Nguema da wasu manyan jami'an gwamnati inda su ka tattauna kan batutuwan sanya hannun-jari. A zaman, an mayar da hankali ne kan yadda masana'antun Ɗangote zasu taimaka wajen haɓaka tattalin arziƙin Gabon ta hanyar samar da masana'antun siminti da taki musamman a ɓangaren samar da albarkatun noma. Nguema ya bayyana jin daɗinsa game da haɗa hannu da…
Read More

An samu tsaiko a shari’ar Kwankwaso kan EFCC

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Sakamakon rashin cike ƙa'idojin babbar kotun jihar Kano da hukumar hana yi wa tattalin arziƙi zagon ƙasa, EFCC ta yi, an samu tsaiko kan sauraron ƙarar da aka shigar kan kare ƴancin shugaban jam'iyyar NNPP, Rabi'u Musa Kwankwaso da wasu mutum bakwai. Jaridar 'Daily Trust' ta ruwaito cewa, waɗanda su ka shigar da ƙarar sun haɗa da; NNPP, Dakta Ajuji Ahmed, Dipo Olayanku, Ahmed Balewa, Cif Clement Anele, Ledi Folshade Aliu, Buba Galadima da kuma Rabi'u Musa Kwankwaso kan hukumar EFCC. A yayin da aka tada batun, lauyan da ya karɓi shigar da ƙarar, Robert Hon,…
Read More
Tinubu ya ɓukaci majalisa ta yi kwaskwarima ga dokar ‘yan sanda da wa’adin sufeto janar

Tinubu ya ɓukaci majalisa ta yi kwaskwarima ga dokar ‘yan sanda da wa’adin sufeto janar

A ranar Talata ne shugaban ƙasa Bola Tinubu ya miƙa wa majalisar wakilai ƙudurin gyaran dokar ‘yan sanda. Ƙudirin dai na neman yi wa wa'adin babban Sufeto Janar na ‘yan sanda gyaran fuska. Shugaban Tinubu ya naɗa Egbetokun a matsayin Sufeton 'yan sanda a watan Yunin 2023 na tsawon shekaru hudu. An naɗa shi tare da sabbin shugabannin tsaro. A cewar sashe na 18 (8) na dokar ‘yan sanda ta 2020, Egbetokun, wanda aka haifa a ranar 4 ga Satumba, 1964, ana sa ran zai yi ritaya a watan Satumba na 2024, lokacin da zai cika shekaru 60 a duniya.…
Read More
Majalisa ta amince da sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000

Majalisa ta amince da sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000

Majalisar dattijai ta amince da ƙudirin N70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi , ta hanyar yin gaggawar zartar da ƙudirin dokar da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya gabatar mata. Ƙudirin dokar wanda ya kuma rage lokacin duba mafi ƙarancin albashi daga shekaru biyar zuwa shekaru uku, an yi karatu na ɗaya da na biyu da na uku a jere a zauren majalisar ranar Talata . Sauran bayanai na zuwa
Read More